Sakataren jam’iyyar New Nigeria People Party (NNPP) a shiyyar arewa maso gabas, Alhaji Babayo Liman, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar tare da shiga cikin jam’iyyar PDP hade da dumbin magoya bayansa.
Ya sanar da cewa, a karkashinsa ya yi rijista wa mambobi sama da miliyan 3.5 a jam’iyyar NNPP a arewa maso gabas cikin shekara takwas, don haka kaso 80 cikin dari na wadannan adadin sun amince da ficewa daga jam’iyyar tare da komawa cikin jam’iyyar PDP.
Liman wanda shi ne Ko’odineta na Kwankwasiyya a jihar Bauchi da Arewa Maso Gabas ya sanar a wani taron manema labarai da ya yi a NUJ da ke Bauchi a ranar Litinin cewa sun yanke wannan shawarar ne domin kishin arewa da ma kasa baki daya.
Ya kuma shaida wa ‘yan jaridan cewa daga cikin wadanda suka fice tare da shi daga NNPP sun hada har da shugabar mata ta shiyyar arewa maso gabas, Hajiya Halima Tafawa Balewa; sakataren watsa labarai na jam’iyyar a shiyyar arewwa maso gabas – Ibrahim Abdu; mamba a kwamitin yakin zaben Kwankwaso – Tijjani Hassan da wasu kusoshin jam’iyyar a arewa maso gabas inda suka sanar da komawa PDP.
Liman ya ce, a jihar Bauchi kawai mambobi da magoya bayansa sama da dubu 700,000 ne suka mara masa baya wajen fita daga NNPP zuwa PDP domin mara wa Atiku da gwamna Bala Muhammad baya.
Liman, ya kara da cewa tun ranar 14 ga watan Janairu ya fice daga jam’iyyar amma ya shelanta wa duniya hakan ne a ranar Litinin bayan yanke matsayar inda ya koma wato PDP, ya nemi sauran magoya bayansu da su biyo shi.
Dakta Babayo Liman sannan ya bukaci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da shi ma kawai ya amince ya koma PDP tare da mara baya wa Atiku Abubakar domin ciyar da kasar nan gaba.
Liman wanda tsohon mamba ne a kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na NNPP, ya ce, “Bisa ga wasu dalilai na kokarin ceto kasar nan daga halin da take ciki, in a da ina cikin duhu ni da magoya bayana sama da miliyan 3.5 a arewa maso gabas yanzu Allah ya bude mana ido mun gane gaskiya.
“Idan muna son gaskiya, muna son arewa muna son Nijeriya, to ya zama dole mu goya baya wa Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar. Wannan shi ne babbar dalilin da ya sa na ga ya kamata na jawo mutane ne sama da miliyan uku da suke arewa maso gabas domin mu goya baya wa Atiku ganin cewa lokacin da Obasanjo ya yi mulki Atiku ne mataimakinsa kuma dukkanin nasarorin da aka samu a gwamnatin Obasanjo Atiku ne sila.”
A gefe guda kuma ya nemi dukkanin magoya bayansa da su mara baya wa Sanata Bala Muhammad a matakin gwamnan jihar Bauchi. Ya nuna kwarin guiwarsa na cewa tabbas Bala Muhammad idan ya zarce zai ci gaba da shimfida kyawawan ayyukan raya jihar Bauchi.
Liman ya kara da cewa muddin jama’a suka zabi Atiku ya tabbata zai yi kokarin magance matsalolin da suke addabar kasar nan da suka hada da matsalar tattalin arziki da tsaro.