Wani dan Nijeriya ya amsa laifin bude asusun ajiyar banki na bogi har guda 470 da ya yi amfani da su wajen damfarar bankunan Amurka da dama.
Ahmed Ponle, dan Nijeriya mai shekaru 42, wanda kasurgumin dan damfara ne, ya amsa tuhumar da ake masa ta damfarar bankuna a wata kotun lardi da ke New Jersey a watan Afrilun shekarar da ta gabata.
Yana fuskantar hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari sakamakon wannan laifi da ya shafi zambar akalla bankunan Amurka 10 da ke kunshe da kudi har Dala miliyan shida.
Alkalin kotun lardin, Noel Hillman, ya sanya ranar 20 ga watan Janairu din nan a matsayin ranar da za a yanke wa Ponle hukunci, bayan jerin dage-dage tun lokacin da ya amsa laifinsa a shekarar da ta gabata.
Masu bincike a Amurka sun bayyana ta wani kundi, yadda Ponle ya yi amfani da fasfunan bogi wajen bude akalla asusun ajiyar banki akalla 470 a rassan bankunan Amurka daban-daban.
Ya yi amfani da fasfunan da ke dauke da hotonsa, amma kuma sunayen bogi ciki har da fasfunan Kenya da Senegal.
Gwamnatin Amurka dai ta tabbatar da cewa, wannan dan taliki bai wahalar da hukuma ba, inda ya amsa laifinsa a ranar 7 ga watan Agustan 2022.