Shugaba Muhammadu Buhari, ya kara wa Babban sufeto na ‘yansandan Nijeriya, Usman Alkali Baba wa’adin aiki, a wata wasika da mahukunta suka fitar kan karin haske akan rade-radin da ake yi na cewa, Alkali zai yi ritaya ne kafin gudanar da zaben ranar 25 ga watan fabrairun 2023.
Ministan kula da harkokin ‘yansanda Mohammed Dingyadi, a jiya laraba ne ya warware zare da abawa akan maganar a ganawarsa da manema labarai a fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartar wa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman.
Dingyadi ya ce, Alkali ba zai yi ritaya a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zabuka a kasar ba, ganin cewa tuni Buhari ya kara wa Alkali wa’adin ci gaba da aikinsa.
Ministan ya ci gaba da cewa, dokar aikin ‘yansanda ta 2022 tuni ta sauya dokokin ritayar Babban Sufeto na ‘yansanda.
Shugaba Buhari ya dai nada Alkali ne mukaddashin Babban sufeto na ‘yansanda a ranar 6 ga watan Afrilun 2021, inda kuma cibiyar ‘yansanda ta kasa, a watan yunin 2021 ta tabbatar masa da mukamin.
A baya Alkali ya kasance yana rike da mukamin DIG kafin ya zama babban sufeto na ‘yansandan.