Garki Abuja wani gari ne mai dadadden tarihi wanda mafi akasarin mutanen da suke cikinsa Hausawa ne da suka fito daga garuruwan Hausawa daban-daban na Arewa.
Mutum da ya shiga shi cikin Garki ya san cewa lalle ya zo inda Hausawa suke kamar yadda masu karin magana ke cewa “da gani babu tambaya”.
- Tabarbarewar Aikin Gwamnati A Matakin Jihohi
- Gina Al‘ummar Sin Da Afirka Mai Koshin Lafiya Ba Batu Ne Na Fatar Baki Ba
Duk irin sarautun da ake da su a kasashen Hausa can ma akwai su kamar irin su Sarkin Aska, Sarkin Fada, Sarkin Fawa, Sarkin Samari, da dai sauran sarautun gargajiya wadanda aka sani.
Wani babban ala’amari game garin Garki shi ne yadda ake gudanar da harkokin kasuwanci, sai mutum ya yi tsammanin kamar ma duk garin kowa dan kasuwa ne. Musamman ma idan mutum ya bi ta wani layin sai zaci kamar yana cikin Kasuwar kantin Kwari na Kano ne.
Bugu da kari, suna da masu dadaddun sana’o’in da aka sans u a garuruwan Hausawa tun fil-azal kamar Dukanci, Kira, Wanzanci da sauransu wanda wani na iya mamakin cewa akwai irin wadannan sana’o’in kuma a tsakiyar Babban Birnin Tarayya Abuja. Babban Sarkin Yanka da Garki ke karkashin masarautarsa shi ne SA’PEYI, DAKTA USMAN NGA KUFI. Wakilinmu IDRIS ALIYU DAUDAWA, ya yi takakkiya zuwa Garki inda ya tattauna da Hakimin Garki wanda har ila yau shi ne Sarkin Hausawan Masarautar Garki, UMARU ABUBAKAR ABDULLAHI wanda ya yi magana ta bakin Sarkin Samarin Garki, ABDULWAHAB MUSA a fadarsa da ke kwaryar Garki kan tarihin kafuwar garin. Ga tsarabar da ya yo wa masu karatu:
Ko za ka fara da gabatar wa masu karatu da kanka?
Sunana Abdlwahab Musa Sarkin Samarin Garki Hausa, tsohon Kansila mai kula da sashen Lafiya da jin dadin jama’a na Karamar Hukumar Birnin Abuja.
Kai-tsaye, mu je ga tarihin Hausawan Garki kamar yadda mai girma Hakimi ya umarce ka ka bayyana wa masu karatu…
In sha Allahu zan yi kokari haka a takaice ba tare da wani bata lokaci ba, domin wani lokaci akwai wasu maganganun kan tarihin da mutane ke samu ya kuma zama sabani da shi. Asalin tarihin Hausawan Garki matafiya ne wadanda za a iya kiran sunansu da Fatake mutanen da ke kasuwanci tsakanin Arewacin Nijeriya da kuma Kudancinta.
Suna tafiya idan suka zo nan wurin da yanzu ake kira da suna Garki suna yada zango wannan tarihi da nake ba ka ya fara ne daga shekarar 1845, tun suna yada zango za ka ga su mutane ne wadanda suke kawo kayayyaki daban-daban suna kuma sayarwa.
Toh, suna sayar da kayayyakin da suka kawo, in sun sayar, in lokacin tafiyarsu ya yi zuwa gida sai su shirya su koma gida, da haka ne har sai aka kawo wani lokaci wanda suka ga yafi dacewa su zauna.
Asalin mutumin da ya fara zama na dindindin a wannan gari da ake kira Garki shi ne Malam Muhammadu na Makarfi, wanda shi ne ya zama Sarki na farko a wannan yanki ko Gari namu wanda mu muka fi kiransa da Garkin Hausa. Ya fara mulkinsa a shekara 1865 Allah ya yi masa rasuwa a shekara ta 1910 ya yi shekara 45 yana mulki.
Daga nan kuma sai Malam Ahmadu wanda ya fara sarautar shi a shekarar 1910, ya rasu a 1925, ya yi shekara 15 yana mulkin, daga nan sai Abdullahi wanda ya fara daga shekarar 1925 zuwa 1938 ya yi shekara13, sai Abdullahi Maje Ruboci daga1938 zuwa 1968 wanda ya yi shekara 30 a kan mulki.
Abubakar Abdullahi shi ne Sarkin Hausawa na biyar har ila yau kuma mahaifin Sarkin Hausa na yanzu ya yi sarauta ne daga 1968 zuwa 2007 ya yi shekara 49. Daga nan nan a jerin Sarakunan Husawan Garki sai Umaru Abubakar Abdullahi shi ne Sarkin Hausawa na yanzu da aka nada shi a shekara ta 2007 Sarki na shida.
Abin da ya faru shi ne mahaifinsa da yaga baya da lafiya sai ya kira shi a matsayinsa na babban dansa, ya kira jama’arsa ya sheda masu ya nada shi a matsayin shi ne Sarkin Hausawa.
Saboda ba ya iya tafiyar da mulki na jagorancin al’ummar Hausawa a matsayin shi na Sarkinsu sanadiyar rashin lafiyar da yake fama da ita, a wancan lokacin da ma shi mahaifin nasa tsohon wanda yake karbar ma gwamnati haraji ne, har daga baya ta zo ta nada shi Dagaci. Lokacin da aka nada shi Dagaci ne sai rashin lafiyar ya yi mashi tsanani, yanzu ma likkafa ta yi gaba saboda an nada shi a matsayin Hakimi na Garki Hausa.
Wasu da yawa suna mamakin yadda aka yi Garkin Hausawa ta samo asali a tsakiyar Al’ummar Gwari (Gbagyi), ko za ka yi karin haske?
Su wadannan Hausawa kamar yadda nake maka bayani daga lokacin da suka fara zama na dindindin al’umma ne wadanda suke da zaman lafiya a tsakanin wadanda suke zama tare. Kuma ita Garki kalma ce ta Arewacin Nijeriya, idan mutane ba su manta ba da akwai Garkin Daura, sai kuma Garki ta Jigawa, ga kuma Garkida, wadda take a cikin Jihar Adamawa.
Kamar dai yadda su al’ummar Hausawa da suke ta tafiye-tafiyen Fatauci, idan suka zo suna daure dabboinsu ne a garke. Da suka yanke shawara ta zama sai suka sa ma garin suna Garki watau ya samo asalin sunan nasa ne daga asalin Garke inda suke daure dabbobinsu, idan sun zo al’amarin Fataucin da suke yi.
Da haka ne Allah ya sa wa garin albarka inda mutane suka yi ta zuwa garin Garki ya samu daukaka, akwai abokan zama wadanda Gwarawa ne kuma su ma ‘yan kasa ne, sai kuma Hausawa su ma ‘yan kasa ne.
Mun ga yanzu baya ga Hausawa da Gwarawa, akwai wasu al’ummomi da suke zama a Garki, me yake janyo hankulansu zuwa nan?
To kamar yadda na yi maka bayani tun farko akwai Shugabanci nagari domin akwai Sarki wanda shi ke gudanar da shugabanci sai mataimakansa da suka hada da Sarkin Noma, Sarkin Fawa, Sarkin Aska, Sarkin Dukawa da dai sauransu. Wadannan mutane su ke taimaka masa duk wanda ya zo su ne za su karbe shi cikin lumana su bashi wurin da zai zauna, da duk wadansu bukatun da yake da su, ba tare da nuna wani bambanci ba na addini ko kabilanci. Mafi yawa dagacikin mutane masu zuwa Garki za ka ga Hausawa ne, saboda sha’awar da jin dadin zuwan da suka yi suka iske ‘yan‘uwansu Hausawa.
Yaya matsayin ilimin yara a wannan yanki na Garki mai tarihi musamman bangaren boko saboda da alama ba a wasa da na addini tun da wuri ne mai tsohon tarihi?
Gaskiya kamar yadda aka dade da sani da al’amarin karatun Boko a Arewa yana fuskantar babbar matsala, domin ba ko wadanne Iyaye ba ne suke amincewa ‘ya’yansu su yi karatun Boko wanda shekarun baya a Arewa an dauki al’marin tamkar wani kafirci ne ilmin zamani ana iya samun ‘yan asalin Garki sun yi karatun. Daga cikin wadanda suke da ilmi mai zurfi akwai wadanda suke da sana’o’in hannu daban- daban, ba sun ce lalle sai sun yi aikin ofis ba, da yawa daga cikinsu sana’o’i ne domin rufa wa kai asiri har ma da taimaka ma wasu.
Ko akwai wani tsari ko tanadi da Hukumar Babban Birnin Tarayya ta yi wa ‘yan asalin Garki ?
Al’ummar da ke zama a nan Garki akwai wurin da Hukumar Babban Birnin Tarayya ta ware masu inda za su koma, wasu ma daga cikinmu tuni sun koma can yayin da kuma wasu ke ganin garin da ya riga ya dade ya fi shekara dari biyu mai dimbin tarihi, bai dace a ce an yi ma shi haka ba. Maimakon haka kamata ya yi a yi hanyoyin zamani da kara samar da abubuwan more rayuwa a cikin Garki tunda ai tsohon gari ne. Akwai kuma wuraren da ita Hukumar Babban Birnin Tarayya ta ware ma Garkin Hausa, Garkin Gwari, Apo, da kuma Ojana.