A jiya Talata 24 ga watan nan ne aka gudanar da taron koli na bakwai, na kungiyar kasashen Latin Amurka da Caribbean, a birnin Buenos Aires, fadar mulkin kasar Argentina.
Game da taron, a kwanan baya ministan harkokin wajen kasar Argentina, kasar dake rike da shugabancin kungiyar a wannan karo Santiago Cafiero, ya zanta da ‘yar jaridar babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG.
A yayin zantawar, Cafiero ya ce, kasar Sin muhimmiyar abokiyar cinikayya ce ta kasar Argentina, kuma Argentina ta shiga cikin ayyukan hadin gwiwa na raya shawarar “Ziri daya da hanya daya”, da zummar inganta zuba jarin da kasar Sin ke yi a Argentina, kuma ko shakka babu, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu za ta samu ci gaba a fagen tattalin arziki da cinikayya, ciki har da manyan ababen more rayuwa, ta yadda za a inganta karfin takara na kayayyakin da Argentina ke fitarwa zuwa kasar Sin, da ma duniya baki daya.
Cafiero ya kuma ce, yana fatan dangantakar dake tsakanin kasashen Argentina da Sin, da ma kasashen yankin Latin Amurka da Sin za ta kara samun ci gaba. Ya ce Argentina ba kawai ta shiga cikin aikin raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” ba ne, har ma ta gabatar da rokon neman shiga tsarin hadin gwiwar BRICS. (Mai fassara: Bilkisu Xin)