Gwamnatin Tarayya ta zargi wasu jam’iyyun adawa da yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari zagon kasa wajen kawo karshen matsalar da ake fama da ita kan kuncin rayuwa sakamakon sauya fasalin Naira.
Lai Mohammed, ministan yada labarai da al’adu, ne ya bayyana hakan a wani taron bayyana nasara gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari (2015-2023) a ranar Talata.
- Zan Tabbatar Da An Ci Gajiyar Man Fetur A Yankin Bauchi Da Gombe Muddin Aka Zabe Ni – Atiku
- Kungiyar Ibo A Jihar Kaduna Ta Nuna Goyon Bayan Ga Sanata Uba Sani
NAN ta ruwaito cewa an shirya taron ne domin nuna irin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu.
A jawabinsa na bude taron, Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi la’akari da irin matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta saboda sauya fasalin kudin Naira da kuma matsalar karancin mai.
A cewarsa, gwamnati na aiki tukuru don daidaita al’amuran da suka shafi tattalin arzikin biyu.
Ya ce abin mamaki ne yadda wasu jam’iyyun siyasa na adawa suka garzaya kotu don hana Buhari da Babban Bankin Nijeriya (CBN) kara wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu ga ‘yan Nijeriya su musanya tsofaffin takardunsu da sababbi.
Mohammed ya ce, “Matakin kotun ya zo ne bayan da jam’iyyun adawa da dama suka yi barazanar kauracewa zaben 2023 idan aka kara wa’adin.
“Wadannan abubuwan ban mamaki da jam’iyyun da abin ya shafa suka yi, wata hujja ce da ke nuna cewa ‘yan adawa sun mayar da wannan batu baki daya zuwa wasan siyasa, inda suka gwammace su sanya ‘yan Nijeriya su kara shan wahala a kan bukatarsu.”
Mohammed ya kara da cewa, “Ta yaya mutum zai iya bayyana gaskiyar cewa wadannan jam’iyyun adawa marasa gaskiya ba sa son wani mataki da zai iya rage radadin da ‘yan Nijeriya ke ciki?.”
Wannan dai na zuwa ne bayan kirayen-kiranye da ake yi wa Buhari da CBN kan irin wahalar da canjin kudi ya jefa ‘yan Nijeriya.