Mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP Datti Baba- Ahmed ya bayyana cewa, babu dan takarar shugaban kasa a zaben shugaban da ke tafe da zai iya samun kuri’a miliyan 1.9 da shugaba Muhammadu Buhari ya samu a zaben 2015 a jihar Kano.
Datti wanda ya bayyana hakan a wata hira ta kai tsaye ta mussaman da gidan talabijin na Channels ta yi dashi akan zaben na 2023 ya ce, Buhari dan takarar jamiyyar APC ya samu kuri’u 1,903,999 da suka bashi nasarar kayar da abokin takararsa na PDP Goodluck wanda ya samu kuri’u 215,779 a kano, jihar da tafi kowacce yawan jama’a.
A cewarsa, tulin kuri’un miliyan 1.9 da Buhari ya samu a jihar Kano a 2015, babu wani dan takarar shugaban kasa da zai yi tunanin iya samun wannan daga jihar.
Datti ya kara da cewa, shiyoyin da za a fafata a lokacin zaben na shugaban kasa sune, jihohin Kaduna da Katsina.
A cewar mataimakin dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar LP, muna samun dimbin goyon bayan jama’a fiye da sauran jam’iyyun.