Jam’iyyar ZLP a Jihar Bauchi, ta bukaci babban lauya, Eko Ejembi (SAN) da abokan aikinsa da su fara shirye-shiryen daukar matakan shari’a kan kwamitin yakin zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP bisa bayyana cewa dan takarar jam’iyyar a Jihar Bauchi, Ambasada Khalid Arewa ya koma PDP tare da janye takararsa.
Idan ba a manta ba a ranar Talata kwamitin yakin zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya ziyarci Jihar Bauchi domin yakin zabensa, inda kusoshi na jam’iyyar ciki har da dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da gwamna Bala Muhammad suka halarta, inda aka bayyana sunayen wasu da suka koma PDP ciki har da ayyana sunan dan takarar gwamna na jam’iyyar ZLP.
- Ya Kamata Amurka Ta Sauya Mahangar Ta Game Da Sin
- Na Yi Alkawari Zan Kawar Da Matsalolin Al’umma, In Ji Tinubu
A hirarsa da LEADERSHIP Hausa a ranar Alhamis, dan takarar, ya karyata labarin, ya kuma nuna bacin ransa tare da cewa kwata-kwata babu wanda ya tuntubesa kan wannan zance.
“Ina zaune a ofis ina ganawa da wasu sai aka fara kirana a waya ana tambayata, ya aka yi aka ji sunana cewa na koma PDP?
“Na ce ban gane ba, wace magana ce wannan?. Wasa gaske na amsa kiran waya kan wannan batun a lokacin sama da 100, inda magoya bayanmu suna nuna takaicinsu da nuna bacin ransu da jin wannan maganar.
“Gaskiya ni ban san da wannan batu ba kuma ba a yi wannan zancen da ni ba. Kuma ba mu shirya cewa zan sauya sheka na koma wata jam’iyya ba.
“Kowa ya ga yadda muka karbu a Jihar Bauchi, babu wani matashi kamata a duk ‘yan takarar nan, ni ne mai karancin shekaru kuma matasa suna alfahari da hakan. Sun kuma shirya wajen ganin nasu ya karbi mulki. Alhamdullahi muna kallon nasara domin tsakaninmu idan har aka yi zabe bisa gaskiya to ni zan ci, sai dai idan magudi za a yi.”
Ya ce, ya fito ya barranta kansa da wannan ikirarin da PDP da ‘yan takaranta suka yi a gaban dubban jama’a.
“Na rubuta wasika zuwa ga babban lauya na kasa kuma muna jiran amsarsa, domin ka san mai neman shugaban kasa zan yi kara Atiku Abubakar da Dino Melaye da ya kira sunana, da kuma shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu, da shugaban PDP na Jihar Bauchi, Hamza Koshe Akuyam.”
Arewa, ya sha alwashin samun nasara a zaben gwamna na 11 ga watan Maris, 2023.
“Wannan bata suna ne baro-baro a matsayina na dan takarar gwamna da nake kallon zan ci zabe, yanzu a sakamakon wannan furucin da suka yi na rasa akalla kashi 30 na magoya bayana.
“Wani daga jin wannan batun shi ke nan ya tafi da shi a ransa ke nan, wani kuma zai ga tun farko yaudararsa aka yi, wani kuma zai ga ban kyauta wa masoyana ba, kowa da yadda zai dauki batun, don haka ba lamari ne da za mu bar shi haka nan ba.”
Arewa ya ce, kwata-kwata babu wata yarjejeniya da suka yi da gwamnatin Jihar Bauchi ko PDP kan cewa zai janye takararsa ba.
“Idan ma za mu janye ya kamata a ji nunfashinmu balle ma hakan baya daga cikin manufarmu. Shin an ma fito an fadi hakan a kan mu don an fi mu cancanta ne ko don rainin da aka mana? Ko kuma a’a fahimtarmu ce ta zo daya, amma babu haka kawai mutum ya tashi kawai ya ce mun janye neman takararmu hakan ba za ta yiwuwa ba.”
A kwafin wasikar da ZLP ta aike wa Lauyoyin ta ce, “Daukan matakin shari’ar shi ne zai dawo wa jam’iyyarmu da kima da mutuncinta kan yarfen da aka mana.”
Wasikar mai dauke da sanya hannun Ambasada Khalid Arewa, dan takarar gwamna na jam’iyyar, “Kwasam a ranar 7 ga watan Fabrairu, 2023 PDP-PCC ya kira sunan dan takarar gwamnanmu a jihar Bauchi, Ambasada Khalid Arewa da cewa ya koma jam’iyyar PDP, wannan furucin ya janyo mana asara sosai da jawo damuwa.”
“Tun lokacin da PDP ta fito ta yi wannan furucin, magoya baya da masoyan ZLP sun shiga damuwa sun kuma nuna rashin jin dadinsu a sassa daban-daban na kananan hukumomin jihar Bauchi.”