A tattaunawar da aka yi tsakanin manyan ‘yan jaridu, Shu’aibu Mungadi, Salihu Dantata, Ibrahim Gamawa, bisa jagorancin Aminu a gidan talabijin na Farin wada da Rediyon Bision, sun tabo al’amuran yau da kullum, da suka addabar Nijeriya, wadanda suka jefa ‘yan kasar cikin wahalhalu, kamar maganar tallafin mai da kudaden da aka kwato daga barayin gwamnati, kalubalen rashin tsaro da sauransu.
Wakilinmu ABUBAKAR ABBA ya saurari tattaunawar kuma ya rubuto mana bisa gudunmawar Shugaban Matasan Arewa Mazauna Legas, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci, kamar haka:
Batun tallafin mai….
Abu ne wanda tun gwamnonin da suka gabata, an sha samun matsalolin ware su bangare daya, inda za a yi handama da kudin da kuma jeka ka ji dadinka ba tare da an yi amfani da da su yadda ya kamata ba, wanda ya zamo abin da yake cutar da gwamnatin.
EFCC ta sha yin na ta kokarin, amma wasu lokutan, ba kwato kudaden ba ne saboda akwai wannan maganar ta dokar ‘yancin samun bayanai wanda wajibi ne wanda ya nemi wani bayani ko na menene aje a nuna masa. Kudaden nan da aka kwato, kafin wadannan me aka yi da su, koke-koke ko zarge-zargen cewa wadansu za su je kafafen yada labarai a zo a gaya mana an kwato daga bayan fage sai a je a yi almubazzanaranci da su.
To yanzu da suka kwato kudaden, sai ga shi Nijeriya ta je tana ranto kudi daga kasashe kamar su China wanda bai kamata ba. To menene mahimmancin kwato wadannan kudaden kuma ba ga wannan kudin tallafin kadai ba, wannan kwato kudin muna ji ne kawai a takarda ba a zahirance ba. Muna son a zo a gaya mana wadanda aka kwato a baya har da na yanzun me aka yi da su?
Ga shi a Nijeriya babu asibitoci ba tsaro ba wutar lantarki da sauransu, mun gaji da kullum a fito ana fifita wa mun kwato ka za, amma ba mu san inda suka shiga ba. ‘Yan Nijeriya na son su sani duk da cewa shi shugaban EFCC bai dade da zuwa wajen ba.
Tun kafin gwamnatin Buhari ta zo, a 2015 ya sha cewe babu tallafin nan olla kawai, almundana ake yi, sai kuma ga shi EFCC ta ce tun da gwamnatin nan ta zo, ta kwato kimanin naira miliyan 13. Ba ka ganin wannan zai zowa wa ‘yan Nijeriya abin mamaki?
Zai zamo masu abin mamaki sosai da wannan Ga dukkan alamu, Buhari bai shirya wa mulkin ba a wancan lokacin kuma bai san abin da ke a cikin mulkin ba, ko kuma ya manta. Da ya dawo abubuwan sun canza. Yadda Bera ke satar daddawa saboda haka da ya zo, yake cewa tallafin man ulmundahana ne ya nuna kamar wani abu ne da babu shi.
To kuma ga shi a lokacinsa, ana ta maganganun cewa, an karbo ko an kwato kudi ka za da ka za, abin da muke son mu sani in an kwato da gaske ne wa kuma aka gurfanar a gaban kotu domin ba su zama halak malak ba, sai kotu ta tabbatar da cewa kudin nan, na alumundahana ne.
Ya kamata ‘yan Nijeriya su dinga tambayar su, ina kudaden nan suka shiga. Su wadanda suka yi sama da fadi da wadannan kudaden na jama’a ai ya kamata a hukunta su, muna son mu sani wanene da wanene a gaban kotu.
Kaga kwanan baya an hukunta tsohon shugaban hukumar fansho Maina kuma ta ce, halak malak a karbo kaya daga gunsa.
To amma wadannan da aka ce an karbo kudaden shin kawai, karbo wa aka yi aka ce na gwamnati ne. Shi ke nan in ka saci kudin gwamnati ba wani hukunci da za a yi maka. Shin wadannan kudaden a wajen wa da wa aka karbo.
Ita EFCC ta yi wa wadanda za su dinga tilasata mata ta yi magana. Saboda haka wannan maganganun da suke fada wa talakawa ba za su gamsu sa su ba, me ya sa yau, ‘yan Nijeriya suke a cikin wahala har yanz, menene amfannin wadannan kudaden fa suke ambata wa. Shi ya sa Nijeriya kullum a wannan gwamnatin ta zama kamar wuta, halin yau, ya fi na gobe kuma duk wadannan kudaden da ake karbo wa jibi ka ji an ce za a karbo bashin tiriliyan ko biliyan ka za, me ya sa maganganun ke sabawa, gwamnati daya ce, amma maganganu sun fi dari, mu ko an karbo ba mu gani a kasa ba, aljihun wa suka tafi, aljihun gwamnati, shi ne take cewa, sai ta ci bashi a waje.
Ba ka ganin wadannan kudaden da gwamnatin ta ce ta karbo duk da cewa ta yi amai ta lashe tun da a da, ta ce babu wannan tallafin daga baya kuma ta zo ta ce akwai wannan tallafin. Me kake gani wannan yake nuni?
Inda za mu zauna, mu zayyano abubuwan na yaudara irin wanda wannan gwamnatin ta yi zuwa yau, zamu iya cewa, yaudarar da wannan gwamnatin ta yi wa mutane da rufa-rufa da aka yi wa mutane, sai daga ba ya kuma abin ya zo ya bayyana ba su da iyaka. Tun kafin a rantsar da shi yake cewa, tallafin nan yaudara ne, sata ce, cuta ce, amma yana shigo wa ya ce zai dakatar da shi. Mutane suna mamakin ka ce babu wannan abun kuma ka ce za ka cire, ke nan akwai shi, sai kuma ya zo ya ce za a kara wa mai kudi saboda tallafin nan yana cin harajin gwamnati da yawa.
A nan kuma EFCC ta ce ta kama kudade na tallafin mai Na bogi wanda ta kwato daga gun mutane, a wannan gwamnatin an san akwai mutanen da ba su shigo da mai ba karya suke yi, amma sai su kawo guntuwar takarda a hada baki da da su da ma’aikatar kudi da ma’aikatar man fetur cewa ni na shigo da mai tan ka za, sai a yi kashe mu raba.
Su wadanda aka kwato kudaden a gunsu, a shanya mana su mu gansu, idan ba a yi hattara ba, sunanan suna yin takarar zabe, ya kamata a yi gyara ga dokokin Nijeriya duk wanda aka kama da cuta kar a bar shi ya ya yi takara, yanzu ga gwamnoni sun cika majalisa, kuma in ba a yi hattara ba, nan da shekaru kazan, za a kai fagen da majalisar za ta kai dari bisa dari na ‘yan majalisar tsaffin gwamoni ne ke ciki. Kuma duk gwamnan da ya yi sata, sai ya yi ritaya ya koma majalisa, su rinka yi wa mutane dokoki, kaga, ba yadda za su yi dokar da za ta rinka kama barawo.
Gwamnatin Buhari tana shigo wa ta fara maganar kudaden badakala na Abacha, aka kuma fara maganar kudaden makamai na Dasuki, a kai ta kama mutane ana yi masu shari’a, ana bata masu suna wasu ma ba su ji, ba su gani ba. Su wadannan jami’an gwamnatin da suka ci kudi, ba za a zo a fito a fada ba, ko dan Bodari baya jin warin jikinsa.
Amma me ya sa EFCC ba ta fito ta yi wa mutane bayani me aka yi da kudaden da aka kama ba?
Ita kanta EFCC tana karkaahin ofishin ministan shari’a ne duk wani mataki sa za ta dauka sai da umarnin ministan shari’a, shi ma yana karbar umarni ne daga gun shugaban kasa, kaga akwai matsaloli, ita dai, ta yi nata aikin, sauran abubuwan da za a yi, ya rage ga shugaban kasa. Ya ce shi bai ma san ko ana bayar da tallafin ba sai da ya shigo, da ya shigo din, menane ya hama shi mayar da abin yadda yake so, kuma mai ya sa yake son gwamnatin da za ta biyo baya, ya Allah ko dai APC ko wata jamiyyar ta ci, me yasa yake son ya yi mata muguntar da zai shafi wata gwamnatin da za ta zo ya tsara yadda tattalin arzikin zai tafi.
Buhari ya dauki alkawura da suka fi shurin masaki yawa kuma har yanzu, ba mu ga ko wanne ba. To me ya sa kuma yake son shiga hurumin wata gwamnatin wanda mun tabbatar in wata gwamnatin ta zo, tana son ta nemi kuri’un talakawa a karo na biyu, to sai ta dauki matakin yadda ‘yan Nijeriya masu jefa kuri’a da wadanda ba sa jefa wa, za su samu sauki a cikin gwamnati.
Cire wannan tallafin a wanne irin hali kake gani, zai jefa ‘yan Nijeriya a ciki?
Daya daga cikin maganganun yaudara na wannan gwamnatin ta zo ta tafi a karshen watan Mayu, amma sai ta ce a watan Yuni za a dakatar da tallafin. Me ya sa gwamnatin Buhari ta ki dakatar da tallafin tun bayan shekaru bakwi da suka wuce. Wato ke nan Buhari na son ya gaya wa ‘yan Nijeriya cewa, tallafin nan da na ce, babu, wanda kuma nace yaudara ne, sata ce, barna ne, ashe gaskiya ce kuma ni na yadda da shi.
Babu kasar da ake zargin jama’arta da sata irin Nijeriya, duk wannan bashin da Nijeriya ke ciwo wa ka duba kaga ina yake fito wa, cibiyoyin nan da ke bai wa Nijeriya bashin, kasashen da ake kai wa kududa ake zargin an sace daga Nijeriya ne, su kuma cikin kudin satar su ranta mana.
Matsalar tsaro an fara ganin sauki sakamakon matakan da gwamnatin ta dauka, amma wannan shekarar kamar Zamfara matsalar na kara dawo wa. Ya ka kalli abin?
Wasu lokutan harkar tsaro ba daga Nijeriya kadai ba, amma na Zamfara da Kebbi da Sakkwato da Nija da wasu yanmunan a arewa maso yamma, abin ya ki kare wa, inda abin ya kafa, mai makon a girke runduna ta musamman a wadannan guraren, sai kuma so dawo, duk da ana zargin akwai hannun wasu jami’an tsaro a ciki da ke bayar da bayanai.
Kana ganin rashin yin amfani da na’urorin fasahar zamani wajen yakarsu shi ya sa abin ya ki kare wa?
Ni a ta wa fahimtar Buhari akwai muskuren da Shagari ya yi, abinda ya yi shine aka mai da sojoji zuwa barki suka zauna ba a yi da su, Anna yanzu an ba su akin yi.
Batun wannan rigingimun, ba za su kare a wannan gwamnatin ba ta Buhari ba, zai ta fi ya bar su, dabaru sun rage wa gwamnatin da za ta zo.