Wani matashi mai suna Salman Umar Hudu, dan shekara 38 dan asalin Jihar Kano ya fada komar Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Zangon Kasa (EFCC).
Jami’an hukumar sun cafke shi ne a wani otal a Abuja, kan zarginsa da yin sojan gona na gabatar da kansa a matsayin shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa.
- Kin Bin Umarnin Kotu Kan Batun Canjin Kudi Zai Iya Kawo Koma Baya – Masana
- An Dawo Da ‘Yan Nijeriya 150 Daga Jamhuriyyar Nijar
Har ila yau, Umar ya kuma kasance yana gabatar da kansa a matsayin ma’aikacin hukumar.
Wanda ake zargin jami’an sun kama shi ne a ranar 14 ga watan fabirairu 2023.
An bayyana cewa, Umar ya karbi Naira 100,000.00 daga gun wani bayan ya bashi tabbacin cewa, yana kula da abubuwa a EFCC.
A cikin sanarwar da EFCC ta fitar a yau Laraba ta ce, Umar na ci gaba da bayar da sahihan bayanai, inda da zarar hukumar ta kammala binciken za ta maka shi zuwa kotu.