Sakamakon sabon tsarin da babban bankin Nijeriya CBN na sauya takardun kudi na naira 1,000 da naira 500 da kuma naira 200 ya jefa ‘yan kasuwa a cikin tsaka-maiwuya, inda suke ci gaba da koka wa, kan asarar da karancin sabbin kudin suka janyo wa sana’o’insu.
Har ila yau, rahotannin sun bayyana cewa, hakan ya kuma janyo faduwar farashin kayan masarufi a kasuwanni sakamakon karancin takardun kudaden a sassan kasar.
- NIS Ta Yi Wa Jami’ai Sama 60 Karin Girma
- Matsafa Sun Kashe Tare Da Cire Sassan Jikin Wani Dalibi A Adamawa
Kusan wannan matsalar ta karade kowanne fannin tun daga fannin hatsi da kuma dabbobi.
Rahotanni sun bayyana cewa, farashin hatsi da sauran kayan abinci sun fadi warwas a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, inda dole ta sa ’yan kasuwar suka fitar da farashin kaya iri biyu farashin mai biya da tsabar kudi daban, na mai biya ta tura kudi.
A kasuwar ta Dawanau, bayanai sun nuna cewa, babban buhun masara da ake sayarwa naira 22,000 a makon jiya ya koma naira 14,000 da tsabar kudi, ko kuma naira 18,000 ga mai biya yin turin kudi.
Bugu da kari, babban buhun gero da ke naira 25,000 a makon da ya wuce kuma ya koma naira 15,000 da tsabar kudi, ko naira 18,000 ga mai tura kudi, inda kuma buhun shinkafa mai buntu mai nauyin 100 kilo kuma ya koma naira 13,000 daga naira 23,000 da aka sayar a satin da ya gabata.
Wasu daga cikin masu hada-hadar hatsi a kasuwar sun bayyana cewa, a kan dole suke sayar da kaya, ko da faduwa za su yi don su samu abin da za su kula da iyalansu.
A cewarsu, rashin takardun kudi ya sa kaya sun karye, ko ma ta wace hanya za a biya.
A jihar Kano a kasuwar kayan gwari ta ‘yankaba kuma, kwandon tumatir da ke naira 8,500 a makon jiya ya koma naira 4,000 saboda rashin ciniki.
A kasuwannin Jos da ke jihar Filato kuma farashin dankali, dankalin taurawa da sauran kayan gwari sun fadi warwas, inda kasuwar Farin Gada da ke Jos, kwandon tumatir da a baya ake sayarwa naira 1,500 zuwa naira 2,000 ya wuce ya koma naira I, 700.
Hakazalika, a kasuwar Maikatako, wadda ta yi fice wajen kasuwancin dankalin turawa a karamar hukumar Bokkos, farashin dankali ya fadi warwas, buhu mai nauyin kilo 50 na dankali ya koma naira 6,500 daga farashinsa na naira 10,000.
A cewar wasu kananan manoma, mu ne muka fi shiga cikin matsala a wannan yanayi, inda suka kara da cewa, a makon da ya gabata a kasuwar kauyen Jamari an sayar da buhu mai nauyin kilo 100 na gero naira 7,000 sabanin naira 20,000 da ake sayarawa a baya.
A bangaren Masara ta koma naira 8,000-naira 10,000 amma kusan babu mai saya; Wake ya koma naira 19,000 daga naira 40,000; abin gwanin ban tausayi, kusan babu wanda bai shafa ba, saboda rashin takardun kudi.
Har ila yau, karancin kudin ta sa rashin ciniki a kasuwar Alaba Rago da ke Jihar Legas, inda ’yan kasuwa ke ta korafi kan gazawar abokan cinikayya wajen samun tsabar kudi don yin sayayya.
A cewar wasu masu sana’ar sayar da kajin da aka sayar naira 10,000 a watan disamba da farkon watan janairu sun koma naira 6000, amma duk da haka babu mai saye.
Wasu ’yan kasuwa a kauyen Oke-Aro da ke kan iyakar jihohin Legas da Ogun sun bayyana irin asarar da suka tafka sakamakon rashin takardun kudaden.
Hakazalika, masu sana’ar sayar da kayan gwari a kasuwar Agbado don sayarwa a Oke-Aro ta bayyana cewa farashin kayan ba su canza ba, amma matsalar ita ce tashin farashin abin hawa, inda wasu tun da aka fara karancin takardun ba ya samun ciniki sosai.
A Jihar Kwara, wata ’yar kasuwa mai sayar da waken suya a karamar hukumar Kaiama, mai suna Amina ta ce lamarin ya sa ba su da zabi sai dai su koma su zauna a gida.
Wata mai sayar da hatsi mai suna Maimuna a Kaiama, ta ce ta bar sana’ar a halin yanzu saboda rashin uwar kudi da kuma abin kula da kanta.
A cewar wata mai shinkafa da wake, Salamat, a Kasuwar Mandate da ke Ilorin ta ce duk da cewa ba asara suke yi a kayan da suke sayarwa ba, matsalar ta rage yanayin cininkinsu da ma harkar hatsi.