Dan takarar majalisar tarayya na Jam’iyyar PDP a karamar hukumar birni, Hon. Injiniya Yusuf Abdullahi Da’awah, ya gwangwaje dalibai 500 ‘Yan asalin Kano Municipal da rabon Jarabawar shiga makarantun gaba da sinkandire ta UTME wacce aka fi sani da JAMB.
An gudanar da taron rabon jarabawar a yammacin ranar Asabar din nan 18, ga Febarairun 2023 a filin taro na kofar gidan Qadiriyya da ke unguwar Kabara mazabar Tudun Wuzirchi a karamar hukumar birni.
- Da’awa Ya Kaddamar Da Shirin Mayar Da Yara 1300 Makaranta Da Rabon Kayan Karatu
- Atiku Ya Kaddamar Da Makarantar Haddar Al-Kur’ani A Kano
A jawabinsa a wurin taron, Injiniya Da’awah, ya godewa Allah bisa wannan dama da ya samu ta daukar nauyin ba wa dalibai 500 JAMB a karo na bakwai bayan rabon Jarabawar NECO da aka yi a baya da rabon kayan makaranta ga ‘Yan Firamare da litittafai da jaka.
Da’awah ya yi wa daliban alkawarin cewa matsawar ya yi nasara a zaben da za a gudanar ranar asabar mai zuwa 25, ga Febarairun 2023 zai dauki nauyin karatunsu har su kammala karatu a Jami’o’in da suka samu gurbin karatu tare da samar musu da aikin yi bayan sun kammala karatun.
Da’awah ya ce, rabon jarabawar ba siyasa a ciki don kuwa babu wanda ya sani cikin daliban, an yada sanarwar ne kawai ta kafafen sada zumunta, su kuma daliban sun cike aka kuma dauke su bisa cancantarsu.
Yusuf Da’awah ya yi alkawarin daukar nauyin yi wa daliban horo kan yadda za su rubuta jarabawar ta JAMB, ya kuma bukaci sauran Jama’a da su yi koyi da wannan tsarin don tallafar ‘ya’yan talakawa.
A nasu jawabin a wurin taron, wasu cikin daliban da suka ci gajiyar shirin, Umar Muhammad da Zainab Hassan Yahaya, sun godewa Da’awah bisa kokarinsa na bayar da tallafin karatun ga dalibai marasa karfi da addu’ar Allah ya kara daga darajarsa.