Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci ‘Yan Nijeriya da su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi dan takarar Jam’iyyarsa ta APC a zaben shugaban kasa da zai gudanar ranar 25, ga Febarairun nan.
Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ga ‘Yan Nijeriya ta hanyar wallafa sakon a shafinsa na kafar sada zumunta na Facebook a yammacin ranar Lahadin nan.
- Ganduje Ya Maka Buhari A Kotun Koli Kan Batu Canjin Kudi
- Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Wa Da El-rufai Martani Kan Zargin Yi Wa Tunibu Zagon Kasa
Shugaba Buharin yabayya cewa, “Zuwa ga ’Yan Nijeriya, ina so in yi amfani da wannan dama domin in sake gode muku da kuka zabe ni har na zama shugaban kasa har sau biyu a jere.”
“A yanzu ni ba dan takara ba ne a wannan zaben, amma jam’iyyata ta APC tana da dan takara wato, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu,”
“Kamar yadda na ambata a baya, Tinubu mutum ne amintacce kuma mai gaskiya mai son Nijeriya, da kaunar ci gaban Jama’a da kasarmu,”
“Ina kira gare ku da ku zabi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Saboda mun gamsu da shi kuma na yi imani zai dora kan irin nasarorin da muka samu,”
“A karshe ina kara tabbatar muku da cewa ina da cikakkiyar masaniyar irin wahalhalun da kuke fuskanta a halin yanzu sakamakon wasu cikin manufofin gwamnati da ake aiwatarwa a yanzu da nufin kawo ci gaba a kasa baki daya,”
“Ina rokon ku da ku kara hakuri yayin da muke daukar matakan da suka dace don rage wahalhalu. In sha Allahu za a samu alheri a karshen lamarin.” a cewarsa.
Yanzu dai abun jira a gani shi ne, shin ko ‘Yan Nijeriya za su amsa kiran na shugaban kasar wurin zabar Tunibun?