Na’urar tantance masu zabe wato BVAS, ta gaza daukan zanen yatsu da hoton fuskar tsohon kakakin Majalisar Dokokin Tarayya, Hon. Yakubu Dogara.
Dogara wanda ya je rumfar zabensa da ke Kauyen Kwarangah da ke karamar hukumar Bogoro a rumfar mai lamba 007 tun wajen 10 na safiya har zuwa 2:pm amma na’urar ta kasa tantance shi balle ya samu damar jefa kuri’arsa.
Lamarin dai ya sanya shi zaman dirshen kawai a wajen zaben da jiran ko na’urar za ta sahaleshi.
Da ya ke zantawa da ‘yan jarida kan wannan matakin, Yakubu Dogara ya nuja takaicinsa na cewa na’urar BVAS guda daya tak ke aiki a mazabar duk da cewa masu zabe sun kusan kaiwa mutum 2,000 a wajen.
Kazalika ya shaida cewar wasu ma da dama na’urar ta kasa tantance su don haka ya yi zargin cewa ana shirin fusata jama’a har su koma gidajensu ba tare da yin zaben ba.
Dogara ya ce, lokacin da ya zo na’urar ba ta tantance shi ba, ya garzaya ofishin INEC da ke karamar hukumar Bogoro domin neman bahasin yadda aka dauki BVAS din Kwaranga zuwa karamar hukumar Tafawa Balewa.
Ya nuna takaicinsa kan yadda al’umma suka bar gidajensu suka fito domin kada kuri’a amma na’urar ta ki tantance su, “Ana ta kan ba da hakuri wa jama’a, to amma muna ganin takaici ne, an ce mana BVAS machine din nan da aka ce ko ma ina ko inda babu network zai yi aiki. Yanzu mun zo an ce ba ta aiki, an dauka an kai Tafawa Balewa, gari da ke da nisan kilomita 12 zuwa 13 daga inda muke a yau don a je a samu network.
“Amma abun da za a lura da shi a nan kasar Kwarangah akwai network masu karfi guda biyu na MTN da Glo. Damuwar mu shi ne meye sa za a dauki BVAS na Kwarangah a kai shi Tafawa Balewa domin a gyara, ko ma network din bai da karfi ai akwai network a Bogoro.
Ya ce, baya ga wannan duk rumfar jefa kuri’ar da ke masu zabe sama da dubu biyu ya kamata a basu BVAS guda hudu, “Amma sun kawo biyu kacal nan duk da masu zabenmu sun kusan dubu biyu. A cikin biyun da suka kawo ma 1 baya aiki. Don haka muna ganin wannan kamar ana son a kular da mutane ne su yi fushi su koma gidaje su ce ba za su yi zabe ba.”
Ya ce za su cigaba da jiran abubuwan da jami’an INEC za su yi domin su na son kada kuri’arsu.
Ya nuna takaicinsa kan yadda na’urar ke cigaba da haifar da koma baya ga zaben.
Daga bisani Dogara ya yi amfani da damar wajen neman jama’a da su yi zabe cikin kwanciyar hankali kuma ya nemi masu takara da su dauki aniyar amsar sakamakon zaben da za a bayyana.