Shugaban kungiyar ‘yan shi’a ta Nijeriya (IMN) Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya bayyana abinda zai yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, idan su ka yi ido hudu.
Sheikh Zakzaky ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC Hausa ta yi da shi Kuma jaridar labarun Hausa ta nakalto.
Da wakikin BBC ya tambaye shi (Sheikh Zakzaky) ko me zai yi idan su kayi ido hudu da shugaba Buhari da gwamna El-Rufa’i, sai ya bayyana cewa:
Zan ce musu su karasa ayyukan da su ka fara, su cika ladan su, na son kashe ni.
Sheikh Zakzaky ya kuma musanta zargin da ake wa mabiyansa na cewa a lokutan muzahara, mabiyan sa na sanya mutane cikin kunci ta hanyar tsare hanyoyi, sai ya mai da amsa da cewa, ba tsare hanya su ke yi ba, amfani su ke yi da ita kamar yadda kowa ke da ‘yanci da damar yin amfani da ita.