Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno, ya kafa wani babban kwamitin bincike mai mambobi 24 kan gobarar da ta tashi a kasuwar Monday Market a ranar Litinin a Maiduguri.
Kamfanin dillancin labarai (NAN) ya rawaito cewa wata gobara mai ban mamaki ta kone gaba daya rukunin kasuwar a ranar Lahadi.
- Lokaci Ya Yi Da Zan Sanya Kowa Farin Ciki A Nijeriya —Tinubu
- Da Dumi-Dumi: INEC Ta Ayyana Bola Tinubu A Matsayin Sabon Zababben Shugaban Kasa
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Shuwa ya fitar a ranar Talata.
Shuwa ya ce kwamitin kuma zai dauki nauyin bayar da agajin gaggawa ga wadanda gobarar ta shafa.
Ya ce sharuddan kwamitin sun hada da tantance musabbabin aukuwar gobarar nan take, domin tantancewa da kuma tabbatar da ko akwai wasu mutane na musamman da ke da alhakin faruwar lamarin kai tsaye ko a fakaice.
Kwamitin a cewarsa, zai kuma duba irin girman gobarar da kuma barnar da aka yi a gine-ginen tare da tantance irin tallafin da za a bai wa wadanda gobarar ta shafa.
Haka kuma za ta tantance ainihin adadin mutanen da suka yi asara tare da tabbatar da adadin dukiyoyin da kowane daya daga cikin mutanen da suka rasa a sanadiyyar gobarar.
Kwamitin yana da Injiniya Zarami Dungus a matsayin Shugaba, yayin da Sakataren Kasuwar Monday Market zai kasance Sakataren Kwamitin.
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ruwaito cewa, gwamnatin Jihar Borno ta fitar da Naira biliyan daya a matsayin tallafi ga wadanda abin ya shafa.
Zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaban manyan makarantu (Tetfund), Kashim Ibrahim sun bayar da gudunmuwar Naira miliyan 100 kowanne.
NAN ya ruwaito cewa kasuwar ta kafu ne kimanin shekaru 35 da suka gabata yayin da kasuwar ta kasance mafi girma a yankin Arewa maso Gabas kuma jigon tattalin arzikin Borno.