Dan takarar shugaban kasa na zaben 2023 a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar zai yi jawabi ga magoya bayansa da ‘yan Nijeriya game da zaben da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.
Atiku zai yi jawabin ne a dakin taro na Yar Adu’a da ke Abuja, babban birnin tarayya da misalin karfe 5:30 na yammacin yau Alhamis.
- Masana Sun Yi Martani Kan Tuhume-Tuhumen Da Ake Yi Wa Alhassan Ado Doguwa
- Buhari Zai Kaddamar Da Aiki Sannan Ya Gana Da ‘Yan Kasuwar ‘Monday Market’ A BornoÂ
Atiku dai ya sha kaye a hannun Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2023.
Tun kafin bayyana sakamakon zaben, PDP da jam’iyyar LP da kuma jam’iyyar ADC sun nesanta kansu daga amincewa da sakamakon zaben da INEC ta ayyanw Tinubu a matsayin zababben shugaban kasar Nijeriya.
Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu, ya sanar a safiyar Laraba, 29 ga watan Maris, 2023, cewa Tinubu na Jm’iyyar APC mai mulki ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar 25 wata.
Bayan tattara sakamakon zaben, Yakubu ya sanar cewa Tinubu ya yi nasara a kan sauran abokan takararsa da kuri’u 8,794,726.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ne ya zo na biyu da kuri’a 6,984,520.
Dan takarar Jam’iyyar LP, Peter Obi, tsohon Gwamnan Jihar Anambra ya zo a matsayi na uku da kuri’a 6,101,533 a yayin da tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya samu kuri’a 1,496,687 a matsayin na hudu.