Hukumar zaben mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC, ta sanar a jiya Laraba cewa, Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya lashe zaben da kuri’u kimanin miliyan 8 da dubu 800. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta bayyana a yau Alhamis cewa, bangaren Sin ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaben. An yi imani cewa, a karkashin jagorantar Tinubu, Nijeriya za ta samu manyan sabbin nasarori.
A gun taron manema labarai da aka saba yi Alhamis din nan, Mao Ning ta jadadda cewa, Nijeriya muhimmiyar abokiyar kasar Sin bisa manyan tsare-tsare ce a cikin nahiyar Afirka. A cikin ‘yan shekarun nan, alakar dake tsakanin Sin da Nijeriya ta bunkasa cikin sauri, kana hadin gwiwa a fannoni daban daban, ya haifar da sakamako mai kyau, wadanda suka kawo alheri ga al’ummar kasashen biyu.
Kasar Sin tana son yin aiki kafada da kafada da sabuwar gwamnatin Nijeriya, wajen karfafa mu’amala da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban, ta yadda za a ciyar da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Sin da Najeriya zuwa wani sabon matsayi.(Safiyah Ma)