Kasar Amurka ta yi kira ga ‘yan takarar shugaban kasa a zabukan da aka yi a makon da ya wuce a kasar nan da su bi hanyar doka domin neman hakkinsu musamman a kan korare-korafen zaben.
Kakakin kasar Ned Price ne ya yi wannan kiran a cikin sanarwar da ya fitar a yau alhamis, inda sanarwar ta ce, akwai matakan shari’a da ya kamata ko wanne dan takara ya yi amfani da su don neman hakkinsa.
- Sin Ta Taya Murnar Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Nijeriya
- Gwamnatin Yobe Za Ta bai Wa Malamai Bashin N500m Don Yi Noma
Sanarwar ta ce, mun fahimci ‘yan Nijeriya da dama da wasu jamiyyun ba su ji dadin yadda sakamakon zaben ya zo masu ba, sun kuma nuna damuwar su akan na’urar da aka gudanar da zaben da ita a karon farko a kasar.
A cewar sanarwar, muna kira ga magoya bayan ‘yan takarar da su guji furta kalaman da za su haifar da rikici a kasar.
Amurka ta kuma yi kira ga The US also (INEC) da ta lalubo da mafita akan matsalar da masu jefa kuri’a suka fuskanta da na’ura BVAS ta zabe kafin zuwan zabukan ranar 11 ga watan maris din 2023.
Sanarwar ta ce, ta kuma samu rahoton kan hare-haren da aka kai wa wasu kafafen yada labarai a lokacin zabukan, inda ta yi kira ga gwamnatin tarayya da jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki a siyasar kasar da sauran ‘yan Nijeriya da su dinga girmama gudunmawar da kafafen yada labarai a kasar ke bayar wa harkar siyasar kasar.
Amurka ta kuma ta ya sabon shugaban kasar da aka zaba Bola Tinubu murna kan lashe zaben.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp