Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad ya yi gargadi da kakkausar murya kan masu neman haddasa fitina a jihar, yana mai cewa ba zai lamunci janyo fitina da tayar wa jama’a da hankali ba.
Bala wanda ke wannan gargadi biyo bayan wani rikicin da ya barke a yankin unguwar Yelwa da ke cikin garin Bauchi a tsakanin bangarorin matasa biyu, inda rikicin ya yi sanadinrasuwar mutum biyu tare da lalata gidaje sama da biyar da kona motoci da mashina da dukiyar jama’a da daman gaske.
- Naira Biliyan 434 Ta Zirare Kan Satar Danyen Mai A Nijeriya
- Wata Yarinya ‘Yar Shekaru 4 Ta Mutu Bayan Ta Faɗa Rijiya A Kano
Bala sai ya yi kira ga al’umar Yelwa da su rungumi zaman lafiya da mutunta juna, ya ce gwamnatinsa na aiki tukuru don tabbatar da inganta zamantakewa da walwalar al’umar jiha, “Don haka ba za mu zura ido wasu tsiraru su kawo mana koma baya kan zaman lafiyar da ake samu a jihar ba.”
Gwamna Bala sai ya yi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar da an zakulo tare da tabbatar da an gurfarnar da wadanda ke da hannun cikin hatsaniyar, inda ya ce kowane rai na da darajar da ya zama wajibi a kare shi.
Daga nan sai ya umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar da ta dauki rahoton asarar da aka tafka tare da samar da tallafi ga wadanda rikicin ya rutsa da su.
Gwamnan ya kara da cewa habaka zaman lafiya nauyi ne dake rataye a wuyan kowane dan jiha.
A gefe guda kuma ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta yi kokarin samar da reshen ofishin ‘yan sanda a yankin Yelwa domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umar yankin.
Gwamna Bala, ya bayar da tabbacin hakan biyo bayan rokon da kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Umar Mamman Sanda, ya yi lokacin da ke yi wa gwamna bayanin abun da ya faru daki-daki.
Kwamishinan ya shaida wa gwamnan cewa, rikicin wanda ya samo asali daga dukan da aka yi wa wani matashi kan sauke budurwarsa daga kan mashin, ya ce sun dauki matakan da suka dace domin tabbatar da hakan bai sake faruwa ba.
Idan za ku iya tunawa dai tun bayan faruwar rikicin matasan da ya hallaka mutum uku a yankin na Yelwa, gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita na tsawon awa 24 a dukkanin unguwar domin tabbatar da kare rayuka da dukiyar jama’a.