A wannan makon mun kawo ra’ayoyinku masu karatunmu a kan karancin kudin da ake fuskanta a yankunan da suke duk da hukuncin kotun koli na a cigaba da karbar tsofaffin takardun kudin 200, 500 da 1000 daga nan zuwa ranar 31 ga watan Disamban 2023.
Yusuf Muhammad Jalingo
Karancin kudi kan yana nan kamar yadda kowa ya sani sai dai abin yana so yabi jikin mutane duk da wahalan da ake fuskanta. Amma ga kotu ta bayar da umarni mukan mun saka na mujiya muga gwamnati za ta bi umarnin kotu ko za ta bijire. Duk dama mun ji wani labari da ake cewa Gwamna CBN yana cewa su sun jima da kona tsoffin takardun naira. Nijeriya mai abun mamaki, Allah ya yi mana mafita.
Kabo Idris Saminu
Ana fama da karancin gudanuwar kudi amma babu wani muhimmacin ace an dawo da tsafin kudade kamar yadda ya kamata shi ne Babban Banki kasa ya dace ya yi shi ne ya wadata bankunan kasuwanci da sabbin kudaden wannan shi ne kawai zai saukaka amma don wahala gaskiya talakawa na wahala kuma kowa ya wasa wukansa abin dai gashi ba’a cewa komai fatan muma zamu yi wa kan mu adalci yanzu mutum sai ya karbi kayan ka kaji shiru.
Bashir Ibrahim Khalil
Mu kam ba a amsar tsohon kudin nan a Ariyanmu amma daman ban dena amsaba har yandu
Aliyu Sulaiman
Duk da hukunchin kotu, nidai a yankinmu babu wani abu da ya canja. Wahalar tsabar kudi bai ragu ba. Tsofaffin ma babu su.
Idan kaje banki ma, ba wani sauyi. Dana je cire N10,000 a kan ‘counter’, tsofaffin N50 aka bani. Duk sun ji jiki.
Abubakar Mohammed Joda
Duk da umarnin kotun koli na cigaba da karban tsoffin takardun kudi, za mu iya cewa ba ta sake zani ba. An rigaya an karbi kudaden mutane kuma bankuna basu samar da wasu sabbi ko tsoffin kudaden da za su ci gaba da kewayawa a cikin al’umma ba. A takaice dai gaba daya tsarin akwai rashin hangen nesa a cikinsa.
Abubakar S G Diso
Abin tambayar anan shi ne me yasa Kashi 95% na yan Nijeriya basu gamsu da hukuncin kotu ba ? idan bera da sata toh daddawa ma nada wari, har yanzu kasuwan mu basu karbar irin kudi, kaga mun bada goyan baya wajen kin aiki da hukuncin kotu kenan
Yusuf Muhammad Jalingo
Karancin kudi kan yana nan kamar yadda kowa ya sani saide abin yana so yabi jikin mutane duk da wahalan da ake fuskanta.
Amma ga kotu ta bayar da umarni mukan mun saka na mujiya muga gomnati zatabi umarnin kotu ko za ta bijire. Duk dama munji wani labari da ake cewa CBN Gomna yana cewa su sunjima da kona tsoffin takardun naira. Nijeriya mai abin mamaki, Allah ya yi mana mafita
Hadiza Bello Hamza
Lamarin karancin kudin kashewa yana nan yana ci wa al’umma tuwo a kwarya, sai dai mu yi addu’ar Allah ya kawo mana sauki