Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jam’iyyar PDP cewa idan ta na da wani ƙorafi to ta garzaya kotu, amma ta daina ƙala wa shugaban ta abin da ta kira “sharri da jingina masa ƙarairayi”.
INEC ta ce maganganun ɓata sunan da PDP ke yaɗawa kan Farfesa Mahmood Yakubu za su iya janyo wa hukumar da shugaban nata su maka PDP a kotu domin su nemi haƙƙin su.
Kakakin Yaɗa Labarai na shugaban, Mista Rotimi Oyekanmi, shi ne ya yi wannan gargaɗi a lokacin da ya ke amsa tambayoyi game da kiraye-kirayen neman shugaban INEC ya sauka daga muƙamin sa.
Oyekanmi ya ce kiraye-kirayen da PDP ta yi kwanan nan cewa Yakubu ya sauka, kawai shirme ne ta ke yi.
Ya ce: “Abin takaici kuma abin dubawa, duk da tulin zargin da PDP ke wa shugaban INEC, waɗanda dukkan su marasa tushe ne ballantana makama, har yau ta kasa kawo hujja guda ɗaya inda ya aikata ba daidai ba, ko inda ya take doka.
“Tabbas, PDP ta kasa kawo ko da hujja guda ɗaya domin bai wa zargin da ta ke yi wata kariya cewa Yakubu ya aikata ba daidai ba ko ya karya dokar zaɓe ta 2022.
“Sannan kuma PDP ba ta bayar da hujjar cewa Yakubu ya yi maƙarƙashiyar ƙin loda sakamakon zaɓe daga na’urar BVAS ba.”
Oyekanmi ya ce abin takaici ne a surutan da PDP ta riƙa yi ba ta ce an yi maguɗi a dukkan sassan da PDP ɗin ta yi nasara a faɗin ƙasar nan ba.”
Kan haka ne INEC ta shawarci PDP idan ta na da wani ƙorafi a kan zaɓe, to ta garzaya kotu kawai.