Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi martani kan wasu batutuwa da wasu mutane ke cewa shi din ya ki cewa uffan kan umarnin da babban kotun koli ta bayar na sake fitar da takardar tsoffin kudi na N500 da N1,000, ya ce, shi babu wani lokaci da ya umarci ministan Shari’a kuma Antoni Janar na kasa (AGF) ko gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) da su ki ko su yi kunnen uwar shegu da umarnin Kotun.
Â
Shugaban ya ce, baya daga cikin dabi’arsa kwata-kwata da ya umarci hadimansa wajen kin mutunta hukuncin kotuna kan lamuran da suka shafi gwamnati da wasu bangarori.
A cewar wata sanarwar da Kakakin shugaban, Malam Garba Shehu da ya fitar a ranar Litinin, ya ce, Buharin tun lokacin da ya shiga ofis a shekarar 2015, bai taba umartar wani mutum da ya yi bore wa umarnin kotuna ba, ya yi imanin cewa demurudiyya ba za ta samu yadda ake bukata ba muddin babu doka.
“Kan halin da ake ciki na batun tsoffin kudade, akwai bukatar jama’a su sani shugaba Buhari bai yi komai wajen kawo cikas ga sashin shari’a ba.
“Bai taka burkin ko hana Antoni Janar da gwamnan CBN daga gudanar da ayyukansu da doka ya tadanar ba. Don haka babu wata shaida da za ta iya nuna cewa shi din ya hana mutanen biyu biyaya ga umarnin babban kotun.
“Shi dai shugaban kasa bayan ganawar da ya yi da Majalisar Kolin kasa. Ya umarci banki da ya tabbatar ya wadatar al’ummar kasa da takardun kudade da suke bukata, kuma babu wani abun da ya canza wannan matsayin nasa.
“Wannan kadai ya ishi al’umma su fahimci cewa shugaba Buhari na matukar mutunta umarnin kotuna.”
Sanarwar ta ce, hatta kesa-kesan da suka shafi cin hanci da rashawa, shugaban baya katsalandan wa harkar shari’a balle ma ya tsoma bakinsa domin yana barin kotuna su yi aikinsu yadda doka ya tanadar.
Garba Shehu ya ce, masu tashi haikan wajen ganin sun bata sunan Buhari da shafa masa kashin kaji na rashin biyayya ga kotu kai tsaye hakan rashin adalci muraran, “Domin babu wani umarnin kotu a kowace gaba da aka yi kai tsaye ga shi ‘Buhari’ a kashin kansa.”
“CBN bai da wani dalilin da zai ki biyayya wa umarnin kotu ya ce yana zaman jiran umarnin shugaban kasa,” Garba ya kara.
Buhari ya kuma karyata jita-jitan da wasu ke yi na cewa gwamamtinsa ta kawo tsare-tsaren da suka ruguza sashin tattalin arziki, yana mai cewa Babu wata gwamnatin da ta fito da tsare-tsare da kyawawan manufofin bunkasa tattalin arziki irin tasa gwamnatin.