An bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dakatar da gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Daraktan yada labaran Bola Tinubu, zababben shugaban kasa, Bayo Onanuga ne, ya yi wannan kiran kan yadda ake ci gaba da fuskantar karanci Naira.
- Mutum 10 Sun Rasu, Da Dama Sun Jikkata A Wani Sabon Hari A Kudancin Kaduna
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran: Kasar Sin Ta Taimaka Wajen Shimfida Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali A Gabas Ta Tsakiya
Onanuga ya ce bai kamata Emefiele ya mamaye ofishin gwamnan CBN ba bayan ya yi watsi da rashin kudi da ake fama da shi.
A cikin wani sakon Twitter, Onanuga: “Na yi mamakin Godwin Emefiele har yanzu yana ofishinsa, ba tare da wata matsala ba, bayan da aka tilasta masa yin watsi da mummunar manufarsa ta sauyin kudi.
“Ya kamata shugaba Buhari ya dakatar da shi daga aiki. Emefiele ya kamata ya tafi yanzu.”
Manufar canjin kudi da CBN ta bullo da shi a watan Disambar 2022 ya janyo wa ‘yan Nijeriya wahala.
Wasu gwamnonin jihohi ne suka fafata da manufar CBN a gaban kotu, kafin zaben shugaban kasa.
Kotun koli ta bayyana cewa tsoffin takardun kudi za a ci gaba da amfani da su har zuwa ranar 31 ga wata Disamba, 2023.