Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnonin jam’iyyar APC da su tabbatar da cewa babban taron da za a yi na zabar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar ya nuna duk wata kima da kyawawan halaye na jam’iyyar.
A wani taro da aka yi a ranar Talata a fadar shugaban kasa, Abuja, shugaban kasar a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar, ya shaidawa gwamnonin 22 da shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, cewa: “ Gaskiya ne an Fara shirye-shiryen gudanar da babban zaben 2023. Nasarar duk wata Jam’iyyar Siyasa ta duniya, tana samun Nasara ne sakamakon hadin kai na ‘ya’yan Jam’iyyar.
“Yayin da na fara shekarar karshe ta wa’adina na biyu a matsayin shugaban tarayyar Nijeriya kuma jagoran jam’iyyar APC, na lura da bukatar da ake da ita na samar da kwakkwaran jagoranci ga jam’iyyar a karkashin wannan tsarin mika mulki da kuma tabbatar da cewa hakan ya faru a cikin jam’iyyar mu. bisa tsari.”
Shugaba Buhari ya ba da tabbacin cewa za a ci gaba da tuntubar juna, domin tabbatar da cewa duk masu son tsayawa takara da masu ruwa da tsaki an fahimci juna, inda ya jaddada cewa hakan zai kuma tabbatar da cewa an shawo kan duk wata damuwa da ta haifar da abubuwa daban-daban.
Da yake jawabi a madadin Gwamnonin Jihohin, Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnoni (PGF), ya ce dole ne jam’iyyar ta ci gaba da samun nasarorin da ta samu a babban taronta na zabukan da ta gudanar a baya-bayan nan, da kuma a zaben fidda gwani da za a gudanar. Don haka, Jam’iyyar zata zakulo dan takarar kishin kasa da kaunar kasa.”
“Za mu goyi bayan shugaban kasa don samun Nasara a babban taron Zaben fidda gwani,” in ji shi.