Yanzu-yanzu muka samu labarin cewa, ɗan takarar Gwamnan Zamfara na Jam’iyyar PDP, Dakta Dauda Lawal Dare ya lashe zaɓen da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata da ƙuri’u 377, 726.
Yayin da shi kuma gwamna mai ci, Muhammad Matawalle ya zo na biyu da ƙuri’u 311, 976.
Dauda Lawal na JamiyyarPDP ya lashe kujerar gwamnan Zamfara
Daga Hussaini Yero
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Dauda Lawal amatsayin zababben gwamnan Jihar Zamfara dan takara Jamiyyar PDP da jimillar kuri’u 377,726, bayan ya doke gwamna Matawalle na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 311,976.
Babban Baturen zaben, Mataimakin Shugaban Jami’ar Birnin Kebbi, Farfesa Shehu Kasimu ya sanar da sakamakon zaben a Ofishin hukumar ta INEC na Jihar Zamfara da ke Gusau a ranar talata cikin dare.
An dai samu tsaiko wurin tattara sakamakon zaɓen bisa kiki-kakar da aka yi ta yi kan sakamakon wasu ƙananan hukumomi wanda PDP ta yi zargin cewa Gwamna Matawalle na yunkurin murɗe zaɓen.
Dauda dare ya lashe mafi rinjayen ƙananan hukumomin jihar ta Zamfara.