Sanata Barau Jibrin ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban majalisar dattawa a majalisa ta 10.
Sanarwar tasa na zuwa ne kwana guda bayan da babban mai tsawatarwar majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya ce lokaci ya yi da zai zama shugaban majalisar dattawa.
- Na Matsu Na Kammala Wa’adin Mulkina -Buhari
- Zaben 2023: Atiku Da Obi Sun Shigar Da Kara Ta Kalubalantar Nasarar Tinubu
Da yake zantawa da manema labarai a zauren majalisar da safiyar Laraba, Sanata Barau ya ce cancanta, iya aiki da gogewa ya kamata su zama abubuwan da za su iya tantance wanda ya kamata ya zama shugaban majalisar dattawa a majalisa ta 10.
Sai dai y ace bai kamata a yi amfani da Addini wajen samar da shugaban majalisar ba.
A cewarsa bai kamata ra’ayin addini ya zama sanadin tantance wanda zai jagoranci majalisar ta 10 ba.
Fafatawar neman mukaman manyan hafsoshin majalisar ta 10 na kara zafafa ganin yadda wasu zababbun ‘yan majalisar tarayya da aka zaba a majalisar dattawa suka nuna sha’awarsu ta tsayawa takara, kuma rahotanni sun bayyana cewa suna zawarcin abokan aikinsu domin neman goyon baya.
Sauran zababbun Sanatoci da suka nuna sha’awarsu na zama Shugaban Majalisar Dattawa sun hada da Godswill Akpabio da David Umahi.