Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana shirin barin gidan gwamnati domin ya koma gidansa, yana aiki a gonakinsa da kiwon dabbobinsa sama da 300.
“Na kosa in bar gidan gwamnati,” in ji Buhari yake bayyana haka a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Talata yayin da yake karbar jakadiyar Amurka, Mary Beth Leonard mai barin gado.
- ‘Yan Nijeriya Sama Da Mutane 39 Ne Suka Mutu A Zaben 2023
- Shema Ya Bai Wa PDP Sa’o’i 48 Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Masa
Ya ce idan aka yi la’akari da damar gudanar da zabe na gaskiya da kuma rashin tsoma baki kamar yadda aka gani a zabukan ranakun 25 ga Fabrairu da 18 ga Maris, ‘yan Nijeriya sun tabbatar da cewa sun iya tantance wanda zai jagorance su ba tare da wani ya gaya musu abin da za su yi ba.
Ya nuna jin dadinsa da gagarumin kishi ga dimokuradiyya da ‘yan Nijeriya ke nunawa ta zabin da suka yi a zaben 2023.
A cewar shugaban, wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar, ya ce da gaske dimokuradiyyar Nijeriya ta girma.
Ya ce: “Mutane sun fahimci ‘yancin da suke da shi. Idan aka ba da damar yin zabe na gaskiya da gaskiya, babu wanda zai iya gaya musu abin da zai yi. Ban ji dadin yadda wasu ‘yan takara suka fadi zabe ba.
“Amma na ji dadin yadda masu jefa kuri’a suka iya yanke zabar ra’ayinsu na wanda zai yi nasara da kuma wanda zai fadi. Duk da canjin kudin na rage zirga-zirgar kudade a hannun jama’a, amma sai da wasu suka raba kudin, na ce wa masu kada kuri’a su karbi kudin su yi zabi ra’ayinsu”
Ya ce ya gamsu da irin rawar da ya taka wajen gudanar da zaben ya tsaya a kansa, ba tare da tsoma baki ko wani tsangwama ba.Ya yaba wa jakadan mai barin gado cewa bisa ga dimbin nasarorin da aka samu a dangantakar Nijeriya da Amurka cikin shekara uku da rabi. Ya bayyana fatan Nijeriya za ta ci gaba da samun ci gaba wajen gina kasa daga cikin al’ummominmu daban-daban da masu fafutuka.
Tun da farko, Leonard ta bukaci a cire tallafin mai ya daga cikin muhimman shawarwarin da Buhari zai iya dauka kafin ya bar mulki a ranar 29 ga Mayu.
Ta ce ta yi farin ciki da irin ci gaban da aka samu a dangantakar Nijeriya da Amurka a cikin shekaru uku da rabi, musamman yadda aka kafa kwanan nan na tsarin bayar da biza na tsawon shekaru biyar tsakanin kasashen biyu, aiki tare a cikin tsaro da samar da kayan aikin soji da suka hada da jiragen yaki da jirage masu saukar ungulu na yaki masu zuwa nan ba da dadewa ba, da kuma hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya don yaki da cutar kanjamau da kuma Korona tare da ba da tabbacin cewa Amurka za ta ci gaba da taimakawa wajen karfafa fannin kiwon lafiya a Nijeriya.
Ta bayyana godiyarta da na gwamnatin Amurka kan ci gaba da rawar da shugaban kasar ke takawa wajen tabbatar da tsaro a yankin Afirka da kuma karfafa tsarin dimokuradiyya a matsayin tsarin gwamnati, inda ta bayyana irin kakkausan martanin da ya bayar kan yawaitar juyin mulkin da aka yi a yammacin Afirka a baya-bayan nan a matsayin wanda bai dace ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp