Rashin fitowar da mata suka yi a zabukan da aka kammala, ya sake haifar da matsala, wanda masana ke ganin zai bukaci a samar da doka mai tsanani a matakin kasa domin wani kaso na musamman da za a kebe wa mata domin nuna adalci.
Wadanda suka zanta da manema labarai sun ce idan aka yi la’akari da bambance-bambancen da Najeriya ke da shi da kuma fafutukar bunkasa dimokuradiyyar da aka fara, mata sun cancanci su ba da gudummuwarsu wajen tsara manufofi a fagen da kuma zartar da hukunci.
A tsawon lokaci, karancin mata a fagen siyasar kasar ya haifar da damuwa a tsakanin masu ruwa da tsaki da masu fafutukar daidaiton jinsi.
A cewar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), mata kusan kashi 47.5 ne cikin 100 na masu rajistar zabe miliyan 93 a zaben 2023 da aka kammala. Sai dai duk da kasancewar mafi yawan al’ummar kasar masu kada kuri’a mata ne amma da kyar suke samun damar zabarsu a mukaman siyasa saboda sabanin da ke tsakaninsu.
Sakamakon binciken da aka gabatar ya nuna cewa wasu mata sun samu kujeru a jihohi 21 – Anambra, Kaduna, Bayelsa, Benue, Kuros Ribas, Delta, Ekiti, Oyo, Taraba, Nasarawa, Filato, Kogi, Kwara, Akwa Ibom, Ogun, Legas, Adamawa , Ondo, Enugu da kuma Ebonyi.
Sai dai ba su yi sa’a ba a Jihohin Bauchi, Borno, Gombe, Imo, Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi, Niger, Abia, Osun, Ribers, Sokoto, Yobe da Zamfara, inda maza ne kawai suka mamaye kujeru.
Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa yankin Kudu maso Yamma ne ya fi yawan mata ‘yan majalisar dokoki da jimillar zababbun mata 16 daga jihohi biyar cikin shida na yankin. Jihar Ekiti ce ke kan gaba da ‘yan majalisa mata 6, Legas da Ondo suna da 3 kowanne, yayin da Ogun da Oyo kowannensu ke da 2. Osun ita ce jiha daya tilo a yankin da babu ‘yar majalisa.
Yankin Arewa ta Tsakiya ya zo na biyu da ‘yan majalisa mata 12 a fadin jihohi biyar cikin shida. Jihar Kwara ce ta zo kan gaba inda ‘yan majalisar mata 5 suka fito, Binuwe, Filato da Kogi kowannensu na da 2, yayin da Nasarawa ta samu 1.
Kididdigar ta kuma nuna cewa shiyyar siyasar yankin Kudu ta Kudu ta samar da mata 10 ‘yan majalisa daga jihohi biyar za su zama na uku. Jihar Akwa Ibom ce ke kan gaba da ‘yan majalisar mata 4, inda Bayelsa da Delta ke da 2 kowanne, Kudu maso Gabas, uku daga cikin jihohi biyar ne suka samar da ‘yan majalisar mata 5. Ebonyi na da 2, Enugu 2, yayin da Anambra ke da guda daya. Jihohin Abia da Imo ba su da ‘yan majalisa mata.
Kamar Kudu maso Gabas, Arewa maso Gabas ma sun samar da ‘yan majalisa mata uku daga jihohi biyu cikin shida na yankin. Yayin da Taraba ta samu 2, Adamawa tana da 1. Sai dai Borno, Gombe, Yobe da Bauchi ba su da ‘yan majalisa mata ko daya.
A shiyyar Arewa maso Yamma, a cikin jihohi bakwai da ke yankin, Kaduna ce ta samar da ‘yan majalisar mata biyu, yayin da jihohin Kano, Zamfara, Jigawa, Sokoto, Katsina da Kebbi ba su da wakilai mata a majalisun dokokin jihar.
Anambra
A cikin jimillar mambobi 30 a majalisar dokokin jihar Anambra, mace daya ce kawai ta iya samun kujerar zama a majalisa.
Misis Nkechi Ogbuefi ta jam’iyyar Labour Party (LP) ta lashe zaben mazabar Anaocha domin dan takarar jam’iyyar PDP Ebele ya yi ritaya. A halin yanzu, mace daya ce tilo a majalisar dokokin jihar mai wakiltar mazabar Onitsha ta Kudu 2, Beberly Ikpeazu, ta gaza komawa majalisar.
Enugu:
A Enugu, Honarabul Gimbiya Obiajulu Ugwu ta lashe mazabar Enugu ta Kudu yayin da Honarabul Jane Ene ta lashe mazabar Udi ta Arewa. A Bayelsa, mata biyu da aka zaba sun haba da Egba Ayibanegiyefa, wacce ta lashe mazabar Yenagoa.
Ebonyi
Ebonyi na da 2, Enugu 2, yayin da Anambra ke da guda daya. Jihohin Abia da Imo ba su da ‘yan majalisa mata. Kamar Kudu maso Gabas, Arewa maso Gabas ma ya samar da ‘yan majalisa mata uku daga jihohi biyu cikin shida na yankin. Yayin da Taraba ta samu 2, Adamawa na da kujera1, sai Misis Ebizi Ndiomu Brown, wacce ta samu nasara a Mazabar Sagbama lll, duk a tutar PDP.
Bayelsa
Jihar Bayelsa na da kujeru 24 a majalisar dokokin jihar, kuma tun daga lokacin ne hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana sakamakon zaben kujeru 23, yayin da har yanzu ba a kammala zabe a mazabar Ogbia ba, yayin da wasu ‘yan daba suka hargitsa zaben a ranar Asabar din da ta gabata.
Benuwe
Jihar Binuwai na da ‘yan majalisa mata biyu a cikin kujeru 30 na majalisar dokokin jihar.
‘Yan majalisar mata sun hada da Misis Lami Danladi wacce ta samu kujerar mazabar Ado a karkashin jam’iyyar APC yayin da Misis Becky Orpin ita ma a karkashin jam’iyyar APC ta lashe mazabar Gboko-East.
Kuros Ribas
A Majalisar Kuros Riba mai mambobi 25, mace daya ce kawai Rita Ayim a karkashin jam’iyyar PDP ta samu wakilcin mazabar Ogoja.
Delta
A Jihar Delta, Marilyn Okowa da Bridget Anyfulu su ne ‘yan majalisar mata biyu da aka zaba a majalisar dokokin jihar.
Marilyn Okowa, wacce diyar Gwamna Ifeanyi Okowa ce ta yi nasara a kan karkashin inuwar jam’iyyar PDP mai wakiltar mazabar Ika ta Arewa maso Gabas. Okowa, wacce a yanzu Marilyn Daramola Gbolahan, ita ce kafin zaben ta ita ce babbar mataimakiya ta musamman kan ilimin yara mata ga gwamnan jihar.
Jihar Bayelsa na da kujeru 24 a majalisar dokokin jihar, kuma tun daga lokacin ne hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana sakamakon zaben kujeru 23, yayin da har yanzu ba a kammala zabe a mazabar Ogbia ba, yayin da wasu ‘yan daba suka hargitsa zaben a ranar Asabar din da ta gabata. Binuwai: Jihar Benue na da ‘yan majalisa mata biyu a cikin kujeru 30 na majalisar dokokin jihar.
‘Yan majalisar mata sun hada da Misis Lami Danladi wacce ta samu kujerar mazabar Ado a karkashin jam’iyyar APC yayin da Misis Becky Orpin ita ma a karkashin jam’iyyar APC ta lashe mazabar Gboko-ta Gabas.
Kuros Riba A Majalisar Kuros Riba mai mambobi 25, mace daya ce kawai Rita Ayim a karkashin jam’iyyar PDP ta samu wakilcin mazabar Ogoja. A Jihar Delta a Jihar Delta, Marilyn Okowa da Bridget Anyfulu su ne ‘yan majalisar mata biyu da aka zaba a majalisar dokokin jihar.
Okowa, wacce a yanzu Marilyn Daramola Gbolahan, kafin zaben ta bayyana kanta a matsayin ‘ yar takara, ita ce babbar mataimakiya ta musamman kan ilimin yara mata ga gwamnan jihar.
Ekiti
A Jihar Ekiti, an zabi Misis Bolaji Egbeyemi Olagbaju, a matsayin mai wakiltar mazabar Ado ta 11, yayin da Okuyiga Eyiyato Adeteju ta lashe zaben mazabar Ayekire/ Gbonyin. Olowokere Bose Yinka, ta samu nasarar wakilcin mazabar Efon, yayin da aka zabi Ogunlade Maria Abimbola a matsayin wakiliyar mazabar Emure. Hakazalika, Fakunle Okiemen Iyabo ta lashe zaben mazabar Ilejemeje, yayin da Abimbola.
Solanke ya lashe kujerar mazabar Moba 1.
Edo
A Jihar Edo, Maria Edeko Omozele ita ce mace daya tilo da aka zaba a majalisar da ta samar da maza 23. Mace daya tilo a majalisar mai wakilai 24 ta lashe zaben a mazabar Esan ta Arewa maso Gabas 11 a jam’iyyar PDP. Ta yi murabus a matsayin kwamishiniyar ci gaban al’umma da jinsi domin tsayawa takarar zaben majalisar dokokin jihar.
Oyo
Jihar Oyo dai na da ‘yan majalisar wakilai mata guda biyu da aka zaba daga cikin kujeru 32. Olajide Olufunke Comforter mai shekaru 47 ce zababbiyar mamba ta farko, wacce ta yi takara kuma ta yi nasara a karkashin jam’iyyar PDP ta mazabar Ibadan ta Arewa 1. Bisi Oluranti Oyewo Micheal daga mazabar Ogbomoso ta Arewa ita ce mace ta biyu da ta yi nasara a tutar jam’iyyar PDP. Ita tsohuwar daliba ce a jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola dake Ogbomoso, kuma tana da digiri na biyu a Jami’ar Ibadan.
Ta kasance mataimakiyar aikin jinya ce a Amurka.
An zabe ta, ta zama ‘yar majalisa ta biyu da za ta wakilci Ogbomoso.
Taraba
Jihar Taraba na da mata biyu da aka zaba daga cikin kujeru 24 na majalisar dokokin jihar.
Hajiya Batulu Muhammed daga mazabar Gashaka ta lashe zaben a karkashin tutar APC yayin da Bonica Alhassan a mazabar Bali ta lashe zaben a karkashin jam’iyyar PDP.
Nasarawa
Jihar Nasarawa tana da ‘yar majalisar wakilai mace daya da ta samu kujera daga cikin 24 da ake da su. An zabi Hajara Ibrahim a karkashin jam’iyyar APC domin ta wakilci mazabar Nasarawa ta tsakiya.
Filato
‘Yan majalisar mata biyu a Jihar Filato sun lashe zaben majalisar dokokin jihar.
Happiness Akawu ta lashe mazabar Pengana, yayin da Salomi Tanimu ta lashe Pankshin ta Kudu, duk a karkashin PDP.
Kogi
A Jihar Kogi, mata biyu ne suka lashe kujeru daga cikin kujeru 25 na majalisar dokokin jihar. Misis Comfort Ojoma Nwuchola ta yi nasara a jam’iyyar APC ta wakilci mazabar Ibaji. An ce ta kasance babbar mataimakiya ta musamman a gwamnati mai ci a jihar kafin ta samu wannan matsayi. Haka kuma, Misis Omotayo Adeleye-Ishaya, ‘yar jam’iyyar APC ta samu nasara a mazabar Ijumu.
Kwara
An zabi mata biyar a majalisar wakilai 24 a Jihar Kwara. An zabi Rukayat Shittu daga Karamar Hukumar Asa a matsayin mai wakiltar mazabar Owode/Onire, yayin da Arinola Lawal daga Karamar Hukumar Ilorin ta Gabas za ta wakilci Ilorin ta Gabas. mazabar. Haka kuma, an zabi Medinat AbdulRaheem daga Karamar Hukumar Moro, ta wakilci mazabar Lanwa/Ejidongari.
Aishat Babatunde-Alanamu ta lashe zaben mazabar Ilorin ta Arewa maso Yamma, yayin da Mariam Aladi ta samu nasara a mazabar Ilorin ta Kudu. Da take magana kan zaben ta, wata ‘yar majalisa.
Rukayat Shittu, ta ce ba za ta iya ba wa mazabarta kunya ba. “Ba dole ba ne in zama mafi kyawu a mazaba na, amma ya kamata in zama mai hikima don in kawo tare mafi kwararrun mutane don yin aiki tare.
Za a jagorance ni da manyan ayyuka hudu na dan majalisa: wakilci, ci gaban majalisa, sa ido kan zartarwa da kuma wayar da kan mazabu, duk da cewa na karshe ba shi ne babban nauyi na bangaren majalisa ba,” in ji ta.
Akwa Ibom
A cikin mambobi 26 a jihar, mata hudu ne suka yi nasarar samun kujeru. Wadanda suka lashe zaben sun hada da Selong Precious Akamba ta mazabar Urua Offong Oruko; Etim Itorobong Francis ta Uruan; Onofiok Kenim Bictor na Oron/Udung Uko da Ukpatu Selinah Isotuk na mazabar Ikot Abasi/ dake Gabashin Obolo.
Wannan karin karuwa ne daga ‘yan majalisar mata biyu da suka zabe su a majalisar dokokin Jihar Akwa Ibom a shekarar 2019.
Ogun
A Jihar Ogun, wasu mata biyu na daga cikin sabbin zababbun ‘yan majalisar 26 da aka zaba. Su ne Bolanle Lateefat Ajayi mai wakiltar mazabar Egbado ta Kudu da Bakare Omolola Olanrewaju ta mazabar Ijebu Ode. Ajayi ta sake komawa majalisar a karo na biyu, yayin da Bakare ya zama na farko.
Ajayi sananniyar malama ce kuma mai taimakon jama’a. An horar da ita a Kwalejin Malamai ta Egbado, Ilaro da Cibiyar Malamai ta Kasa (NTI/DLS), Kaduna, Ilaro campus, Jihar Ogun.
A baya ta yi aiki a matsayin malamar aji, mataimakiyar babban malami.
Adamawa
A Adamawa Kate Raymond Manuno (PDP) ta lashe zaben wakiltar mazabar Demsa a majalisar dokokin jihar. An fara zabe ta a 2019, sannan aka sake zabe a 2023. Ondo
A Ondo, mata uku ne suka lashe kujerun majalisar wakilai a zaben da ya gabata.
Su ne Witherspoon Atinuke Morenike (Mazabar Owo I), Fayemi Olawunmi Annah (Mazabar Ilaje), da Ogunlowo Oluwaseun (Mazabar Idanre).
Mutanen uku wadanda dukkaninsu ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki ce, na cikin ‘yan majalisar wakilai 26 da aka zaba a karshen mako.
Ebonyi
A Ebonyi, daga cikin kujeru 24, mata ne suka samu nasara a mazabu biyu na jihohi. Wadanda suka yi nasara su ne Misis Esther Agwu da Chinyere Nwagbaga a tutar APC na Ohaukwu Mazabar Arewa da Ebonyi Arewa maso Gabas.
Kaduna
A Kaduna mata biyu ne suka samu kujeru a majalisar dokokin jihar. Misis Comfort Amwe ta jam’iyyar PDP ta lashe zaben mazabar Sanga, yayin da Munira Suleiman Tanimu ta APC ta lashe zaben mazabar Lere ta Gabas. Amwe ita kadai ce mace a jihar Kaduna Majalisar tun daga zaben 2019 kuma an sake zabar ta a karo na biyu a jam’iyyar PDP.
Da take magana kan fitowarta, Munira Tanimu ta ce za ta mayar da hankali ne kan ilimi, karfafa mata da matasa. Ta ce akwai bukatar a tallafa wa mata da ‘ya’ya mata domin su shiga harkokin siyasa.
Wadannan su ne matan da suka samu nasarar lashe zaben majalisun jihohinsu a zaben 2023 da gudanar.
Zababben Sanatan Babban Birnin Tarayya Abuja, ya shaida wa kafar Daily Trust ranar Asabar cewa abin bakin ciki ne a ce adadin mata a majalisar dattawa ya ragu zuwa uku, “Gaskiya muna bukatar mu ga yadda za mu samu amincewa da wannan doka.
“Na shirya samun mata da yawa a cikin tsarin jam’iyyar. Zan tallafa wa mata don samun tikitin zama masu ba da shawara. A cikin 62, muna bukatar a kalla 25. Don haka, a cikin jam’iyyata, za ku ga babban ci gaba a yawan mata a wannan yanki a fagen siyasa,” in ji ta.