Tsohon dan wasan ungiyoyin Manchester United da Barcelona, da AC Milan da Inter Milan da Jubentus da Ajad da kuma PSG, Zlatana Ibrahimovic, ya karya tarihin tsohon mai tsaron ragar asar Italiya, Dino Zoff, na wanda ya buga wasa da yawan shekaru.
Tawagar asar Sweden ta sha kashi da ci 3-0 a gida a hannun Belgium ranar Juma’ar data gabata a wasan farko a rukuni na shida a neman shiga Euro 2024 da za a buga a Jamus.
Dan wasa Romelu Lukaku ne ya ci wa Belgium kwallo uku rigis a wasan farko da Kebin de Bruyne ya fara aikin kyaftin din tawagar, bayan maye gurbin Eden Hazard, wanda yayi ritaya.
Bayan kammala gasar kofin duniya a Katar da Belgium ba ta taka rawar gani ba, Hazard ya sanar da yin ritaya, ya mayar da hankali a kungiyar kwallon afa ta Real Madrid.
Zlatan Ibrahimovich ya buga wasan ya kuma karya tarihin da Dino Zoff ya kafa kusan shekara 20 a matakin mai shekaru da yawa da ya buga wasanni a tarihin kwallon kafa a duniya.
Zoff ya kafa bajintar ranar 29 ga watan Mayun shekara ta 1983 a karawar Sweden da Italiya, wanda ya buga wasan yana da shekara 41 da kwana 90 sannan Ibrahimovich ya buga fafatawar ta ranar Juma’a yana da shekara 41 da kwana 172, yayin da tsohon golan Italiya ya yi wasan yana kusan cika shekara 40 da haihuwa.
Sweden ta gayyaci Ibrahimovich, domin buga mata wasa, bayan shekara daya rabon da ya buga mata wasa bayan ya yi ritaya da buga wa Sweden wasa bayan kamala gasar Euro 2016 daga baya ya koma buga wasa a shekarar 2021, inda asar ta kasa samun tikitin shiga kofin duniya a atar a 2022.
Ibrahimovic, ya buga wa AC Milan wasa uku a bana, fafatawa ta arshe da ya yi wa Sweden ita ce da Poland da suka yi rashin nasara a neman zuwa kofin duniya da aka yi a atar.
Tsohon dan wallon shine kan gaba a ci wa Sweden wallaye a tarihi mai 62 a wasa 121 sai dai kuma ranar Juma’a Girka ta je ta doke Gibralta 3-0 a wasan farko a rukuni na biyu a neman shiga Euro 2024.
Lee Casciaro ya buga wa Gibralta wasan yana da shekara 41 da kwana 176, kenan shi da Ibrahimovich suka kafa tarihin masu yawan shekarun haihuwa da suka buga wasan a tarihi kenan.