Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) reshen Jihar Taraba ta sanar da daukar matakin shiga yajin aiki na yajin aiki.
Hakan ya biyo bayan izinin da shugabannin kungiyar ASUU na kasa suka bai wa reshen jihar na fara yajin aikin domin biyan bukatunta da kuma rashin amincewar gwamnatin jihar na biyan albashin ma’aikata.
- Tsohon Mataimakin Sakataren NUJ Zai Kai INEC Kotu Kan Zaben Gwamnan Jihar Kaduna
- Saura Wasanni 10 Arsenal Ta Lashe Kofin Firimiyar Ingila
Kungiyar ta bayyana dalilin da ya sa suka dauki matakin, wanda ta ce ya ta’allaka ne a kan gazawar gwamnatin jihar wajen biyan alawus-alawus din karatu, basussukan karin girma da biyan albashi ga ma’aikata da kuma tsarin fansho na ma’aikata da ba a daidaita su ba.
Mista Samuel Shitaa, shugaban kungiyar ASUU na Jami’ar Jihar Taraba, ya bayyana cewa, sauran dalilan da suka sanya suka dauki matakin sun hada da rashin aiwatar da yarjejeniyae da aka kulla a baya.
Da yake mayar da martani kan yajin aikin, gwamnatin jihar ta bakin kwamishinan ilimin manyan makarantu, Edward Baraya, ya ce har yanzu kungiyar ba ta sanar da matakin da ta dauka ga gwamnatin jihar ba.
Ya yi mamakin dalilin da ya sa ASUU za ta dauki irin wannan matakin yayin da gwamnati mai ci ke yin duk mai yiwuwa don magance matsalolin kafin barin mulki a ranar 29 ga Mayu.
Shi ma da yake mayar da martani, mai bai wa gwamna Darius Ishaku shawara kan harkokin yada labarai, Bala Dan-Abu, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya jaddada cewa gwamna mai barin gado bai bar bashin albashin ma’aikata ba.