Kasar Amurka ta gudanar da taron koli na demokuradiyya na shugabannin kasa da kasa karo na biyu tun daga ranar 29 zuwa 30 ga wannan wata. Akwai wani sharhin da aka rubuta cewa, taron kolin ya yi kama da wasan kwaikwayo na raba duniya.
Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, taron kolin ya shaidawa duniya ma’auni biyu da Amurka ta ke amfani da shi kan batun demokuradiyya.
Mao Ning ta bayyana cewa, burin Amurka na gudanar da taron kolin shi ne raba kasashen duniya cikin kungiyoyi bisa ma’aunin kasar, da tsoma baki kan harkokin kasa da kasa domin moriyarta.
A cewarta, batun ya sabawa tushen demokuradiyya, da tsarin demokuradiyya kan dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da kuma ka’idojin kundin tsarin mulkin MDD, lamarin da zai yi illa ga kasa da kasa wajen tinkarar kalubale tare.
Har ila yau, ta ce batun ya shaida cewa, Amurka ta mai da hankali ga moriyarta ne kadai, a kokarinta na mayar da sauran kasashe ‘yan amshin shataci, kana ta sabawa tsarin demokuradiyya, wato wata daraja ta dan Adam baki daya. (Zainab)