Da takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, a zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, ya ce ba zai tsoma baki a gwamnatin Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ba.
Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam’iyyar NNPP na kasa kuma ake kallonsa a matsayin uban gidan Abba, ya ce idan gwamna mai jiran gado ya nemi shawararsa, zai ba shi.
- Elon Musk Ya Zarce Barack Obama Yawan Mabiya A Twitter
- Saura Wasanni 10 Arsenal Ta Lashe Kofin Firimiyar Ingila
Wasu dai na ta nuna fargabar cewa Abba ba shi da cikakken ikon tafiyar da mulkinsa, inda suke zargin Kwankwaso ne zai ke juya akalar gwamnatinsa.
Sai dai a wata hira da ya yi da BBC Hausa, tsohon gwamnan na Kano, ya ce a matsayinsa na dan Kano, zai yi adawa da sabuwar gwamnati a duk lokacin da ya ga ta yi ba daidai ba.
Ya ce, “Idan ya nemi shawararku ku ba shi, amma idan bai tambaya ba, to ku yi shiru.
“Lokacin da nake gwamna na yi aiki da wasu mutane ciki har da Abba wadanda suka taimaka min wajen samun nasarar da na samu.
“Saboda haka muka zauna muka kalli mutanenmu duka muka zabi wanda muke tunanin idan Allah ya kai mu ba zai maimaita barnar da Ganduje ya yi ba.
“Dukkanmu a Jihar Kano mun yi farin ciki da Allah ya kori gwamnatinsu, kuma muna addu’ar Allah ya nesanta mu da su. Duk wanda ke mulkin Kano, ko soja ne ko wane ne, ba za mu bar shi ya ci mutuncinsa ba.
“Don haka ko Abba ne yake mulki ko wane ne, za mu gaya masa duk abin da ya dace, idan kuma ba ya yi ba daidai ba, nan za mu gaya masa.
“Abin da na sani shi ne cewa za a gyara duk abubuwan da aka yi ba daidai ba a lokacin gwamnati mai barin gado.”