Gwamnatin Kano ta ja hankalin zababben gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, da ya daina fitar da sanarwa da sunan shawara ga jama’a har zuwa lokacin da zai karbi mulki.
A cewarta, irin wannan shawara za ta iya haddasa shakku a jihar.
- Boao: Kasar Sin Ta Karfafa Gwiwar Kasa Da Kasa
- Elon Musk Ya Zarce Barack Obama Yawan Mabiya A Twitter
Wannan na cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Muhammad Garba ya fitar wajen yin martani ga ofishin ga zababben gwamnan a kan su guji gini a filayen gwamnati.
Gwamnatin Kano ta ce abin da zababben gwamnan ya yi na bayar da umarni a kan wani batu da ya shafi manufar gwamnati, daidai lokaicn da gwamna mai ci har yanzu ke kan mulki, tamkar neman shiga sharri ba shanu ne.
Ta kara da cewa kamar yadda yake kunshe a cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya, Abdullahi Umar Ganduje zai ci gaba da zama gwamna mai cikakken iko har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, kuma yana da damar gudanar da ayyukansa har zuwa ranar saukarsa daga mulki.
A ranar Alhamis ne dai gwamnan mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf ya fitar da wata sanarwa wadda ya bayyana a matsayin shawara, inda ya yi kira ga masu gine-gine a filayen gwamnati, ciki har da Masallatai, makabartu da makarantu da su dakata tsagaita.
Sai dai wasu kiran na sabon zababben gwamnan bai yi musu dadi ba, inda aka dinga cece-ku-ce a kafafen sada zumunta.