Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ta ƙaddamar da cibiyar bayar da ingataccen fasfo na zamani da za ta karaɗe jihohin Edo da Delta.
Hukumar ta ƙaddamar da cibiyar ce a ranar Talatar nan bisa jagorancin Ministan Cikin Gida Rauf Ogbeni Aregbesola da Shugaban NIS, CGI Isah Idris Jere.
Sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na NIS, ACI Amos Okpu ya fitar, ta bayyana cewa, da yake ƙaddamar da cibiyar, Minista Aregbesola ya ce cibiyar za ta dinga biyan buƙatun masu neman fasfo da suka fito daga yankunan jihohin Edo da Delta.
Ministan ya ƙara da cewa, cibiyar za ta kasance ta musamman da za ta kula da ofishoshin fasfo na jihohin guda biyu, saboda ƙara inganta ayyukan samar da fasfo a waɗannan jihohi.
Ya ƙara da cewa bisa ƙaddamar da cibiyar, ofisoshin fasfo na jihohin Edo da Delta za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran wurare da ke yankin kudu maso gabas da kudu maso yamma wajen samun nasarar bunƙasa ɓangaran fasfo na zamani.
Minstan ya ce inganta fasfo na zamani wata dama ce da masu buƙatar za su zaɓi nau’in fasfo da suke muradi, kamar mai feji 32 da ke aiki na tsawon shekaru biyar da mai feji 64 da ke aiki na tsawon shekaru biyar da kuma mai feji 64 da ke aiki na tsawon shekaru 10.
Ya ce inganta harkokin fasfo zuwa na zamani hanya ce ta ƙara bunƙasa fasaha, musamman inganta sha’anin taro ta yadda kundayen hukumar da ke ɗauke da bayanai za su yi wahalar kwaikwayo da buga na jabu.
A cewarsa, an samar da wannan cibiya ce domin sauƙaƙa wa masu neman tare da kauce wa wahalar da su zuwa wuri main isa a duk lokacin da suka buƙaci samun fasfo, ta yadda za su yi amfani da na’urar zamani wajen gabatar da buƙatarsu ta samun fasfo cikin kwanciyar hanhali a gidajensu ko kuma a ofishinsu.
Ministan ya jaddada cewa gwamnati tana ƙara wasu shirye-shirye wajen tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya suna samun fasfo cikin sauƙi ba tare da wata wahala ba.
A nasa jawabin, Kwanturola Janar na Hukumar NIS, Isah Jere Idris ya bayyana cewa samar da cibiyar ingantaccen fasfo na zamani da ke Benin na ɗaya daga cikin ƙoƙarin sauye-sauyen da yake aiwatarwa a ɓangaren, musamman wajen ƙara faɗaɗa wa masu neman fasfo hanyoyin samu da kuma zaɓi a kan irin wanda suke muradi.
Ya buƙaci masu neman fasfo da su ziyarci shafin hukumar na intanet a passport.immigration.gov.ng a kowani lokaci, domin biyan kuɗaɗe da kuma gabatar da buƙatar neman fasfo tun kafin lokaci ya ƙure, domin kaucewa cunkoso lokacin da suke buƙata.
Ya ƙara da cewa hukumar ba ta amince da biyan tsabar kuɗi ba, inda ya yi kira da masu nema da su tabbatar sun biya kuɗaɗensu ta shafin intanet tun kafin su ziyarci ofisoshin fasfo lokacin da aka tsara musu.
Tun da farko dai, Gwamnan Jihar Edo, Mista Godwin Noheghase Obaseki ya yaba wa hukumar NIS bisa samar da waɗannan sauye-sauye wajen bayar da fasfo. Ya nuna jin daɗinsa wajen zaɓar garin Benin a matsayin cibiya ta wannan aiki, inda ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta bayar da duk wata gudummuwa da hukumar take buƙata ciki har da tabbacin goyon bayan ƙudurin aikin gina ofishin fasfo a Auchi.
Bugu da ƙari, Sarkin Benin, Mai Martaba Omo no’ Oba n’Edo Uku Akpolokpolo, Oba Ewuare II, Ogidigan ya yaba wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bisa amincewa da kafa cibiyar ingantaccen fasfon na zamani a masarautarsa. Ya ƙara da cewa shugaban ƙasa ya daɗe yana faranta wa mutanen Jihar Edo rai da kuma ‘yan Nijeriya gaba ɗaya.
Ya tabbatar da cewa zai bayar da goyon baya kan wannan aiki tare da miƙa godiyarsa ga Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola bisa jagorantar manyan jami’an hukumar NIS da kuma sauran ma’aikatu da suka zo yankinsa.
A cikin waɗanda suka halarci ƙaddamar da katafariyar cibiyar ta fasfo har da Hon. Justice PA Akhikhero wanda ya wakilci Alƙalin-alƙalai na jihar, da shugaban ma’aikatan gwamna da muƙaddashin shugaban jami’ar Ambrose Alli, Farfesa Osarheme Osadolor, da shugabannin rundunar sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro.