Mutanen yankin Mai’adua ta Jihar Katsina na kokawa kan matsalar gyaran masallaci da ta dame su tsawon lokaci.
Al’umar yankin sun ce a baya sun yi wannan koke kan matsalar babban masallacin juma’ar nasu da ke ƙaramar hukumar Mai’adua yanzu ma suna sake miko kokon bararsu kan dai wannan matsalar.
“Muna masu ƙara miƙa ƙoƙon bararmu ga illahirin masu hannu da shuni ‘ƴan siyasa da sauran masu niyya da su zo su bayar da rance ga Allah (S.W.A), su taimake mu wajen gyaran masallacin mu don girman Allah.”
Wannan masallacin da kuke gani ya ɗauki tsawon shekaru sama da goma ba tare da an duba matsalolinsa ba, kuma shi ne babban masallacin Juma’a na Izala na ƙaramar hukumar Mai’adua.
Allah yasa ya a dace.