Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta ce fasinjoji mata uku ne suka mutu yayin da wasu fasinjoji 13 suka samu raunuka a lokacin da wata motar haya bas ta haya ta kama wuta a ranar Talata.
Kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano.
- Ramadan: Hisbah Ta Rufe Wuraren Shan Giya, Ta Hana Karuwanci A Jigawa
- Shirin Mika Mulki: Buhari Da Gwamnoni Za Su Sake Bayyana Kadarorinsu
Ya ce motar hayar kirar Toyota Hiace mai lamba XE 222 TRN ta kama da wuta a kusa da Kwalejin Fasaha ta Gwamnati da ke Karamar Hukumar Nassarawa ta Jihar.
Ya ce lamarin ya faru ne yayin da motar bas da ta fito daga karamar hukumar Ajingi zuwa Kofar Wambai ta kone kurmus.
Sanarwar ta ce jami’an kashe gobara da jami’an hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) sun yi nasarar kashe gobarar tare da samun nasarar ceto wasu fasinjojin.
Abdullahi, ya ce wasu mata uku da ke cikin motar bas din sun kone ta yadda ba za a iya gane su ba, ya bayyana sunayensu a matsayin Surayya Umar da Zeenai Babaji.
Abdullahi ya ce sauran 13 da suka samu raunuka an kai su Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, domin yi musu magani.
Ya ce an kuma ceto direban motar mai suna Muhammed Gali mai shekara 35 da kwandastan motar, Hassan Danladi mai shekara 30 ba tare da wani rauni ba, sannan aka mika su ga ‘yan sanda don yin bincike.
Kakakin ya alakanta musabbabin hatsarin da keta haddin gudu da kuma fashewar tayar motar ta baya, ya bukaci masu ababen hawa da suke yin tuki cikin taka-tsan-tsan.