Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci Majalisar Dattawa ta amince da wani kudurin dokar kare bayyanai wanda sashen zartarwar gwamnatin tarayya ya gabatar a Majalisar.
Kamar yadda dokar kasa ta tanadar a sashi na 58 sakin layi na 2 na kundin tsarin mulkin Nijeriya wanda aka yi wa kwaskwarima a 1999.
- Gwamnatin Kaduna Ta Sassauta Dokar Zirga-Zirga Da Ta Saka A Wasu Yakuna
- Hukumar NAFDAC Ta Bankado Magunguna Marasa Rajista Na Naira Miliyan 15 A Abuja
Shugaban ya bayyana wannan bukatar ne cikin wata wasikar da ya aike wa Majalisar wanda aka karanta a zaman da Majalisar tayi a ranar Talata.
A cikin wasikar, shugaban ya ce “Na gabatar da wannan kudiri na dokar kare muhimman bayyanai ta Nijeriya a gaban wannan Majalisar domin ta yi nazari a kai kana ta tabbatar da shi a matsayin doka”
Makasudin samar da wannan doka shi ne domin kare hakkin ‘yancin ‘yan kasa ta yadda ya shafi bayyanansu kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadar.
Manufar dokar ita ce samar da tsarin dokar kariyar bayyanai mutane da kuma kafa hukumar kare bayyanai ta Nijeriya da za ta sa ido a kan dokokin bayanan jama’a.
Daga cikin wasu muhimman abubuwan da dokar ta kunsa, akwai batun tsarin yadda za a rinka sarrafa bayyanan mutane, inganta tsarin yadda za a gudanar da bayyanan mutane ta hanyar da za ta kare tsaron bayyanan nasu da kuma samar da sirranta masu bayanan da kuma tabbatar da an mu’amalanci muhimman bayyanan da adalci, ta hanyar shari’a.
Baya da hakan, dokar za ta taimaka wajen kare bayyanan mutane da kuma samun wani abun dogaro idan an samu sabani a bangaren bayanan mutane, tabbatar da cewa, masu kula da bayannan sun yi wa mutane adalci a game da bayyanansu.
Idan ba a manta ba, a shekarar 2022 ne shugaba Muhammadu Buhari ya ba da amincewarsa wajen kafa cibiyar kula da muhimman bayannani wanda Dokta Vincent Olatunji ya ke jagoranta a matsayin kwamishana domin tabbatar da an bi tsarin kare muhimman bayyanai na Nijeriya.