Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce harin da aka kai kan cocin garin Owo na jihar Ondo makonni biyu da suka gabata ya girgiza al’umar kasar nan, da kuma kashe-kashe da garkuwa da mutane a karshen makon da ya gabata a jihar Kaduna, ya bayyana cewa akwai wani shiri da miyagun mutane suke yi na sanya kasar cikin rikicin addini.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da lamarin cewa “ ‘yancin addini da bambancin da muke da shi, shi ne ya sa Nijeriya ta zama mai girma. Irin wannan bambancin ne ke baiwa Nijeriya karfinta. Shi ya sa makiya Nijeriya ke neman ruguza ta, ta hanyar saka mu gaba da juna.
- Harin Jirgin Kasa: Wajibi Ne Mayar Da Fasinjojin Da Aka Sace Gidajensu A Raye —Buhari
- ‘Yan Bindigar Da Suka Kai Wa Maniyyata Hari A Sakkwato Sun Kashe ‘Yan Sanda 6
“Ba za mu kyale su ba. Al’uma ba za ta wargaje ko raba kawunansu da wadannan munanan laifuka da ake shirya wa a fili da shigar da siyasa ba.
“Masu aikata laifin matsorata ne; raunana kuma miyagun mutane masu dauke da bindigogi suna kashe mutane, cikin ruwan sanyi, suna kashe mata da yara marasa makami a wuraren ibadarsu”.
“Za a hukunta su kan laifukan da suka aikata. Za mu gurfanar da su gaban kotu.
“Ina kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su hadu mu yi addu’a, Kirista ko Musulmi kuma mu taimakawa wadanda abin ya shafa da iyalansu.
“Mu nunawa makiya da ke neman raba kan mu ta hanyar addini cewa ba za a raba mu ba. Mu nuna musu cewa ’yan Nijeriya za su ci gaba da tare da mutunta bambance-bambancen juna.” Cewarsa.