• Leadership Hausa
Tuesday, June 28, 2022
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Ba Zamu Zura Idanu Ana Kai Hare-hare Coci Ba —Buhari

by Muhammad
5 days ago
in Labarai
0
Jerin Sunayen Sabbin Ministocin Da Buhari Ya Aike Wa Majalisar Dattijai Ta Tantance Su
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce harin da aka kai kan cocin garin Owo na jihar Ondo makonni biyu da suka gabata ya girgiza al’umar kasar nan, da kuma kashe-kashe da garkuwa da mutane a karshen makon da ya gabata a jihar Kaduna, ya bayyana cewa akwai wani shiri da miyagun mutane suke yi na sanya kasar cikin rikicin addini.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da lamarin cewa “ ‘yancin addini da bambancin da muke da shi, shi ne ya sa Nijeriya ta zama mai girma. Irin wannan bambancin ne ke baiwa Nijeriya karfinta. Shi ya sa makiya Nijeriya ke neman ruguza ta, ta hanyar saka mu gaba da juna.

  • Harin Jirgin Kasa: Wajibi Ne Mayar Da Fasinjojin Da Aka Sace Gidajensu A Raye —Buhari
  • ‘Yan Bindigar Da Suka Kai Wa Maniyyata Hari A Sakkwato Sun Kashe ‘Yan Sanda 6

“Ba za mu kyale su ba. Al’uma ba za ta wargaje ko raba kawunansu da wadannan munanan laifuka da ake shirya wa a fili da shigar da siyasa ba.

“Masu aikata laifin matsorata ne; raunana kuma miyagun mutane masu dauke da bindigogi suna kashe mutane, cikin ruwan sanyi, suna kashe mata da yara marasa makami a wuraren ibadarsu”.

“Za a hukunta su kan laifukan da suka aikata. Za mu gurfanar da su gaban kotu.

Labarai Masu Nasaba

Alaramma Sadeeq Umar Da Ya Wakilci Nijeriya A Musabakar Al-qur’ani Ta Tanzaniya Ya Rasu

2023: INEC Ta Kara Wa’adin Yin Rajistar Katin Zabe

“Ina kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su hadu mu yi addu’a, Kirista ko Musulmi kuma mu taimakawa wadanda abin ya shafa da iyalansu.

“Mu nunawa makiya da ke neman raba kan mu ta hanyar addini cewa ba za a raba mu ba. Mu nuna musu cewa ’yan Nijeriya za su ci gaba da tare da mutunta bambance-bambancen juna.” Cewarsa.

Tags: BuhariHarin coci
ShareTweetSendShare
Previous Post

Majalisar Malaman Musulunci Ta Oyo Sun Nada Ganduje Sarautar ALAUDDEN Na Yarbawa

Next Post

‘Yan Sandan Burtaniya Sun Cafke Ike Ekweremadu kan Zargin Amfani Da Sassan Jikin Wani Yaro

Related

Alaramma Sadeeq Umar Da Ya Wakilci Nijeriya A Musabakar Al-qur’ani Ta Tanzaniya Ya Rasu
Rahotonni

Alaramma Sadeeq Umar Da Ya Wakilci Nijeriya A Musabakar Al-qur’ani Ta Tanzaniya Ya Rasu

9 hours ago
2023: INEC Ta Kara Wa’adin Yin Rajistar Katin Zabe
Labarai

2023: INEC Ta Kara Wa’adin Yin Rajistar Katin Zabe

10 hours ago
Dubun Wadanda Suka Kwakwule Idon Wani Yaro A Bauchi Ta Cika
Al'ajabi

Dubun Wadanda Suka Kwakwule Idon Wani Yaro A Bauchi Ta Cika

11 hours ago
An Kashe Kasurgumin Dan Fashin Dajin Da Ya Addabi Mutane A Leren Jihar Kaduna
Labarai

An Kashe Kasurgumin Dan Fashin Dajin Da Ya Addabi Mutane A Leren Jihar Kaduna

11 hours ago
Rikicin Kabilanci: An Fara Binciken Wasu Manyan Sarakuna A Kogi
Labarai

Rikicin Kabilanci: An Fara Binciken Wasu Manyan Sarakuna A Kogi

12 hours ago
Buhari Ya Rantsar Da Ariwoola A Matsayin Sabon Alkalin Alkalai Na Kasa
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Sace DPO A Kaduna

12 hours ago
Next Post
‘Yan Sandan Burtaniya Sun Cafke Ike Ekweremadu kan Zargin Amfani Da Sassan Jikin Wani Yaro

'Yan Sandan Burtaniya Sun Cafke Ike Ekweremadu kan Zargin Amfani Da Sassan Jikin Wani Yaro

LABARAI MASU NASABA

Alaramma Sadeeq Umar Da Ya Wakilci Nijeriya A Musabakar Al-qur’ani Ta Tanzaniya Ya Rasu

Alaramma Sadeeq Umar Da Ya Wakilci Nijeriya A Musabakar Al-qur’ani Ta Tanzaniya Ya Rasu

June 27, 2022
2023: INEC Ta Kara Wa’adin Yin Rajistar Katin Zabe

2023: INEC Ta Kara Wa’adin Yin Rajistar Katin Zabe

June 27, 2022
An Gudanar Da Gasar Harshen Sinanci Ta Chinese Bridge Ga Daliban Jami’a Da Na Sakandare A Uganda

An Gudanar Da Gasar Harshen Sinanci Ta Chinese Bridge Ga Daliban Jami’a Da Na Sakandare A Uganda

June 27, 2022
Dubun Wadanda Suka Kwakwule Idon Wani Yaro A Bauchi Ta Cika

Dubun Wadanda Suka Kwakwule Idon Wani Yaro A Bauchi Ta Cika

June 27, 2022
Kasar Sin Za Ta Kara Zuba Jari A Fannin Muhallin Halittu

Kasar Sin Za Ta Kara Zuba Jari A Fannin Muhallin Halittu

June 27, 2022
An Kashe Kasurgumin Dan Fashin Dajin Da Ya Addabi Mutane A Leren Jihar Kaduna

An Kashe Kasurgumin Dan Fashin Dajin Da Ya Addabi Mutane A Leren Jihar Kaduna

June 27, 2022
Rikicin Kabilanci: An Fara Binciken Wasu Manyan Sarakuna A Kogi

Rikicin Kabilanci: An Fara Binciken Wasu Manyan Sarakuna A Kogi

June 27, 2022
Buhari Ya Rantsar Da Ariwoola A Matsayin Sabon Alkalin Alkalai Na Kasa

‘Yan Bindiga Sun Sace DPO A Kaduna

June 27, 2022
Yawan Kwararru Masana Kimiyya Da Fasaha Na Kasar Sin Ya Karu Zuwa Miliyan 112 Da Dubu 341

Yawan Kwararru Masana Kimiyya Da Fasaha Na Kasar Sin Ya Karu Zuwa Miliyan 112 Da Dubu 341

June 27, 2022
Kasar Sin Na Adawa Da Duk Wani Yunkuri Na Bata Sunan Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”

Kasar Sin Na Adawa Da Duk Wani Yunkuri Na Bata Sunan Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”

June 27, 2022
ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.