Daga cikin ’yan takarar mataimakan gwamna mata 24 a jihohi 15 da suka samu damar tsayawa takara tare da ‘yan takarar gwamnoni maza, an zabi guda shida kacal kamar yadda sakamakon zaben gwamnan na ranar 18 ga watan Maris ya bayyana da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar.
A jihohi 28 da aka gudanar da zaben gwamnoni a kasar nan, 15 daga cikin wadannan jihohin da mataimakan gwamnoni mata a jam’iyya daya ko sama da haka, wanda ya kawo adadin mataimakan mata da suka tsaya takara zuwa 24.
Duk da cewa ba a bayyana sakamakon zabe na jihohi guda biyu daga cikin jihohi 28, wanda ya hada da Adamawa da Kebbi, kasancewa hukumar INEC ta ce zaben bai kammala ba, an dai sanar da sakamako daga jihohi 26. A halin da ake ciki, INEC ta sanya ranar 15 ga Afrilun 2023 za a sake gudanar da zaben cike gibi a jihohin Kebbi da Adamawa.
A cikin wannan rahoto, jaridar Daily Trust a ranar Lahadi ta bayyana zababbun mataimakan gwamnonin mata shida.
A jihohi 19 na Arewa, jihohi biyu da suka hada da Kaduna da Filato na da mataimakan zababbun gwamnoni mata.
Dr Hadiza Balarabe Sabuwa (Kaduna)
Hadiza Sabuwa Balarabe ‘yar siyasa ce kuma kwararriyar likita wacce ta zama mataimakiyar gwamnan Jihar Kaduna tun daga shekarar 2019. Ita ce mace ta farko da aka zaba a matsayin mataimakiyar gwamnan jihar, an zabe ta tare da gwamna Nasiru el-Rufai a 2019 a karkashinta tutan jam’iyyar APC mai mulki.
An haife ta a gidan Alhaji Abubakar Balarabe a karamar hukumar Sanga da ke Jihar Kaduna.
Hadiza ta yi karatun sakandire a makarantar mata da ke Soba, sannan ta yi digiri a jami’ar Maiduguri, inda ta karanci fannin likitanci a 1986.
Ta kuma kasance babbar sakatariyar hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar kafin ta zama mataimakiyar gwamna Nasir El-rufai a shekarar 2018.
Hadiza Sabuwa Balarabe ta karbi takardar shaidar cin zabe daga INEC tare da zababben gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani a ranar Juma’a da ta gabata.
Josephine Piyo (Filato)
Misis Josephine Piyo ita ce mataimakiyar zababben gwamnan Jihar Filato. Ta tsaya takara a karkashin jam’iyyar PDP tare da zababben gwamna, Caleb Mutfwang.
Piyo ta kasance fitacciyar ‘yar siyasa ce a jihar, kuma tsohon shugaban karamar hukumar Riyom na Jihar Filato, ta kasance tsohowar ‘yar majalisar dokokin Jihar Filato. Mutfwang ya ce zabin Piyo shi ne batun ba da ‘yanci ga kowa.
Piyo ta kasance ma’aikaciyar lafiya ce kuma ta yi aiki a matsayin ma’aikaciyar gwamnati daga baya ta fada harkokin siyasa gadan-gadan.
Hakazalika, a shiyyar Kudu maso Kudu na kasar, mata biyu ne suka zama mataimakan gwamnoni.
Dr Akon Eyakenyi (Akwa Ibom)
Dr Akon Etim Eyakenyi ita ce mataimakiyar zababben gwamnan Jihar Akwa Ibom a karkashin jam’iyyar PDP.
Eyakenyi, wanda ita ce Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Kudu a Majalisar dattawa, a halin yanzu kuma ita ce mataimakiyar shugaban kwamitin ilimi na majalisar dattawa.
Ta fara gwagwarmayar siyasa ne a shekarar 2000, a matsayin kwamishiniyar masana’antu, kasuwanci da yawon bude ido a lokacin mulkin Obong Bictor Attah.
A shekarar 2013, tsohon Gwamna Godswill Akpabio ya nada ta shugabar hukumar makarantun fasaha ta Jihar Akwa Ibom, sannan ta zama ministar filaye da gidaje da raya birane a shekarar 2014 a lokacin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan.
A watan Yunin 2015, an nada Eyakenyi a matsayin kwamitin fasaha na tashar ruwan tekun Ibaka, sannan a watan Oktoban 2016 an nada ta matsayin shugabar majalisar gudanarwa na kwalejin kimiyya da fasaha ta Jihar Akwa Ibom da ke Ikot Osurua. Ta ta auri Injiniya Etim Eyakenyi, dan asalin Ikuita a karamar hukumar Oron.
Dr Ngozi Nma Odu (Ribas)
Dakta Ngozi Nma Odu, Farfesa ce a fannin abinci da kiwon lafiyar jama’a a jami’ar PAMO na Kimiyyar Likitanci da ke Fatakwal. Farfesa Odu ta kuma taba yin aiki a jami’ar Fatakwal a matsayin malama a sashen nazarin ilmin halitta da kuma matsayin babban darakta na riko na farko na gidauniyar jami’ar Fatakwal. Sannan kuma farfesa ce da ke karantarwa a jami’ar Jihar Ribas.
A matsayinta na ma’aikaciyar gwamnati a jihar, ta kasance tsohuwar babbar sakatariyar ma’aikatan lafiya ta Jihar Ribas, mukamin da ta rike na tsawon shekaru shida da rabi (1999 – 2006), inda ta kasance babbar sakatariya a wannan ma’aikata.
Ta yi wa kasar hidima ta hanyoyi daban-daban. Ta nazarci manufofin kiwon lafiya bugu na biyu har sau uku a 2004. Ta sake duba shirin sashin lafiya na 2004 – 2007 na (FMOH). Ta kuma yaba da aiwatar da shirin hadin gwiwa na kamfanoni masu zaman kansu da gwamnati a kan harkar kiwon lafiya a Jihar Akwa Ibom a shekarar 2005. Ta samar da daftarin tsarin bunkasa kiwon lafiya na jiha (SSHDP) ga Jihar Bayelsa a 2009 a matsayin mai ba da shawara ga FMOH. Ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara ga SPDC, TOTAL, NLNG da UNDP.
A yankin Kudu maso Yamma kuwa, mataimakiyar gwamna mace daya ce ta fito daga zaben gwamnan da aka kammala.
Engr Noimot Salako Oyedele (Ogun)
Injiniya Noimot Salako-Oyedele ita ce zababbiyar mataimakiyar gwamnan Jihar Ogun. Ita ce mace daya tilo mataimakiyar gwamna a yankin Kudu maso Yamma kafin zaben gwamna Biodun Oyebanji na Jihar Ekiti a bara, wanda ke da mataimakiyar mace, Misis Christianah Afuye.
An haifi Salako-Oyedele a shekarar 1967 a cikin iyalan Marigayi Farfesa Lateef A. Salako, a karamar hukumar Ado Odo Ota ta Jihar Ogun.
A matsayinta na injiniya, tana da kwarewa sama da shekaru 30 a fannin tuntubar juna, kwangila da kuma sassan gidaje.
Ta kasance a cikin hukumar gudanarwa na kamfanoni da dama a Nijeriya da Birtaniya, kuma a halin yanzu tana aiki a matsayin babban jami’in gudanarwa na kamfanin ‘Glenwood Property Development Company Limited’.
Ta yi digiri na biyu a fannin kiwon lafiyar jama’a daga kwalejin kimiyya da fasaha da ke Landan, sannan ta yi digiri na farko a fannin injiniya a jami’ar Jihar Legas.
Salako-Oyedele ta zama mace ta uku a matsayin mataimakiyar gwamnan jihar bayan zaben gwamna Dapo Abiodun a shekarar 2019. An sake tsayar da ita takara kuma ta lashe zabe karo na biyu tare da Abiodun a zaben ranar 18 ga watan Maris.
A yankin Kudu maso Gabas, Jihar Ebonyi ce kadai aka zabi mace a matsayin mataimakiyar gwamna.
Patricia Obila (Ebonyi)
Patricia Obila ta kasance mataimakiyar shugabar karamar hukumar Afikpo ta Arewa a har karo na biyu. An zabi Obila a matsayin mataimakin zababben gwamna, Honarabul Francis Ogbonnaya Nwifuru, an bayyana ta a matsayin wacce ta kammala karatun digiri da gogewa a harkar shugabanci.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa mata mataimakan gwamnoni a kasar nan sun samo asali ne tun lokacin mulkin soja a shekarar 1990, lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya nada mata biyu mataimakan gwamnoni a jihohin Legas da Kaduna.
A jihar Legas akwai, Modupe Okunnu ita ce mace ta farko mataimakiyar gwamna da ta yi aiki a karkashin gwamnatin Birgediya Janar Raji Rasaki (rtd).
A wannan shekarar ne aka nada Aisha Pamela Sadauki a matsayin mataimakiyar gwamna a Jihar Kaduna a karkashin gwamnatin Abubakar Tanko Ayuba (rtd).
Tun a wancan lokaci mata ke zama mataimakan gwamnoni a jihohi da dama, duk da cewa har yanzu ba a zabi kowacce mace a matsayin gwamna ba. Jihohi kamar Legas, Osun, Ogun, Ekiti, Anambra, Filato, Kaduna na cikin jihohin da suka sami mataimakan gwamnoni mata.
A halin yanzu, jihohi hudu ne kawai ke da mataimaka mata a kasar. Su ne Cecilia Ezeilo a Jihar Inugu da Hadiza Balarabe a Kaduna da Noimot Salako-Oyedele a Jihar Ogun da kuma Ipalibo Gogo a Jihar Ribas.
Duk da cewa ana ci gaba da samun mataimakan gwamnoni mata a kudancin kasar nan, har yanzu arewacin Nijeriya na baya kan wannan lamari.
Farfesa Kamilu Sani Fagge, wani manazarcin siyasa daga jami’ar Bayero da ke Kano, ya bayyana cewa al’ada da addini na daga cikin abubuwan da ke shafar harkokin siyasar mata a Arewacin Nijeriya.
Ya ce “Muna da al’ada a Afirka cewa mata ba a ganin su a cikin jama’a wanda ke ba da karin matsayi ga maza, kuma wannan yana ba wa matan wani nau’i na hana su fitowa takara. Sun gwammace a ba su wasu kaso na mukamai,” in ji shi.