Yayin da yawan ‘yan Nijeriya ke karuwa kullum sai ga shi kuma kwararrun ta banagen kiwon lafaiya suna kara raguwa,saboda kuwa yadda tsarin kula da marasa lafiya yakamata ya kasance kamar yadda kudurin hukumar lafiya ta duniya ya bayyana na Likita daya ya lura da marasa lafiya 1,000 yanzu al’amarin ya kasance ne na likita 1 ya duba marasa lafiya 10,000 a Nijeriya
Yadda kwararrun da suka shafi kula da lafiyar al’umma suke barin Nijeriya hakan ba karamin cikas yake kawo ma bangaren kula da lafiyar al’umma ba, yanzu kalilan wadanda kware a bangaren kula da lafiyar al’umma suke rage a Nijeriya,domin su kula da lafiyar ‘yan Nijeriya.
- Sallah: Gwamna Bagudu Ya Umarci A Biya Albashin Watan Afrilu
- INEC Ta Raba Muhimman Kayyayakin Zabe Don Kammala Zaben Gwamnan Kebbi
Alkalumman da ake dasu sun nuna Nijeriya ta rasa fiye da Likitoci 9,000 da suka barta zuwa kasashen Ingila, Kanada, da kuma Amurka tsakanin shekarun 2016 da 2018.Hakanan ma Likitoci 727 wadanda suka kware a Nijeriya suka koma Ingila kadai cikin wata shida, tsakaniu watannin Disamba 2021 da Mayu 2022.
Alkalumman da aka samu daga cibiyar kula da aikin Nas da Unguwar zoma ta Ingila ta nuna ‘yan Nijeriya da aka koya masu suka kware daga aikin, ya nuna wadanda suke barin sun karu da kashi 68.4 ko daga2,790 a watan Maris na 2017 zuwa 7,256 na watan Maris 2022.”
Da yake tabbatar da hakan shugaban kungiyar Likitoci na kasa (MDCAN),yace bada dadewa ba Nijeriya tana daukar kawi Likitoci kashi 30 na 4000 da ake yayewa ko wace shekara a Nijeriya.Kamar yadda shugaban na kungiyar ta Likitoci, Doctor Bictor Makanjuola cewa yayi, “Muna daukar kashi 30 daga cikin wadanda muka sake horarwa 4,000 ko wace shekara”
Makanjuola ya ce muna daukar kashi 30 na kwararru wadanda muke sake horarwa duk da yake Nijeriya ta sake shiga cikin matsalar za kuma ta cigaba da fuskantar hakan, har sai idan an dauki matakan daya kamata.
Ya kara jaddada cewa “Idan muka dauki kashi 30 na 12,000 hakan shi yafi fiye da kashi na4,000.idan kuma muka horar dai 12,000,kashi 30 shi yafi kyau fiye da wadanda ake dasu a halin yanzu na kusan 4,000.Da hakan mu kesa ran taimaka ma shi al’amarin ba kamar yadda ya dace ba amma a kalla dai ana cigaba da yin tsarin.”
Halin da ake ciki yanzu dokar hana hana Likitoci da Likitocin Hakora barin Nijeriya ta tsallake karatu na biyu a zaman majalisarWakilai ta kasa, har sai sun yi shekara biyar.
Kudurin dokar wanda Ganiyu Abiodun Johnson ya gabatar mai taken, “ Kuduri mai niyyar ayi gyara a dokar Likitoci da Likitocin Hakora ta kasa, mai lamba ta Cap M379,ta dokokin Nijeriya shekara ta 2004 domin yin duk wani gyara domin a sa duk wani wanda ya aka horar a matsayin Likitan Hakora ko Likita sai ya yi shekara biyar tukuna kafin a amince ma shi wajen bashi cikakken lasi wanda kungiyar ce zata bada,wannan duk domin a samar da kulawa da lafiyar ‘yan Nijeriya kamar yadda ya dace (HB.2130).
Sai dai kamar yadda ya jaddada Makanjuola cewa yayi “ Hakane shi al’amarin kwararru ta bangaren lafiya yake a kowacce kasar duniya abin ba ya tsaya bane kan Likita,Ko Nas- Nas,da Unguwar-zoma ba,har ma da daukar hotunan wasu cututtuka, da dai sauransu.Duniya tana bukatar kadan daga cikin masu nagarta.
“Babu wanda zai bari don saboda da kishi kasa kadai zai ki zuwa wurin da za a rika biyan shi har sau goma fiye da abinda ake biyan shi,bayan wannan ma akwai wadansu abubuwa masu bada kwarin gwiwa, sai kuma mutum ya tsaya wurun da ba za a biya shi abinda ya dace ba,wani lokaci abin yayi kasa sosai.Matsalar da muke fuskanta ke nan wannan shi yasa muke ba gwamnati shawara ta kara inganta sharuddan aikin Likitoci da sauran ma’aikatan lafiya,yayin da ta bangaren namu muna yin abinda ya dace na kara yawan wadanda muke horarwa da yaye su.”