Ranar Sallah rana ce wadda take cike da farin ciki musamman ma karamar Sallah kamar yadda mutane ke cewa ko kuma Idil- fitir za ayi ta ne bayan an yi Azumin watan Ramadan kwana ashirin da tara ko talatin,bayan an dawo daga Sallah Idi mutane manya da yara, maza da mata an shiga bukukuwan Sallah ke nan wadanda sanin kowa ne sun bambanta. Ana iua Sallah ko ranar Jumma’a ko Asabar idan an yi Azuni 29 ko 30 kamar yadda tun farko aka dauri niyar.
Kamar yadda na fara yin bayani kan shagullan da ake yi ranar Sallah domin nuna farinciki sun bambanta daga wannan zuwa wancan, abin ya danganta ne kan wane irin shagali ake son ayi.
- INEC Ta Musanta Zargin Bangaranci A Zaben Adamawa
- Sin Ta Samarwa Kasashen Waje Tallafin Ayyukan Likitanci Ba Tare Da Sharudan Siyasa Ba
Yayin da wasu suke nasu shagalin da bai wuce makadi da rawa ba,wasu abin nasu ya yi matukar wuce ka’ida domin kuwa bayan ba a unguwar da suke ba ko garin da suke, suke yin shagalin Sallar ba,wasu tafiya suke takanas ta Kano har zuwa wata unguwa ko wani gari domin su sheke ayarsu saboda acan ba su kusa da wanda ko wadanda za su rika taka masu burki.
Akwai dai maganar yadda ake amfani da abubuwan hawa da suka hada mota ko mashin ayi mugun gudun daya wuce ka’ida wanda idan ba sa’a aka yi ba ana iya yin mummunan hadari da zai kasance ya yi sanadiyar samar da wata nakasa,rauni,ko mutuwa da wasu ko wani za su iya samun kansu a ciki. Wadannan abubuwan duk ana cikin hankali ne ake tunanin yinsu har a kai ga shiga halin da za a nemi hankalin a rasa gaba daya.
Wasu gungun matasan ko ba su tafi wani wuri ba a unguwar tasu su kan wuce makaki da rawa saboda kuwa shan kayan maye kamarsu Wiwi giya,muggan kwayoyi sai abinda hali yayi don haka akwai bukatar Magidanta ko Iyaye baki daya daga mazan har matan su sa ido kan abubuwan da ‘ya’yansu za su iya yi marasa kyau da sunan wai bukuwan Sallah.