Yayin daya rage kwana ma gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu kwana 43 ta kammala wa’adinta na biyu abinda ya kai shekara takwas ke nan,fadar Shugaban kasa ta cigaba da kare shi inda take jinjina ma shi kan ayyukan cigaban da yayi.
Mai ba Shugaban kasa shawara na musamman akan yada labarai da wayar da kan al’umma Femi Adesina,ya ce Muhammadu Buhari ya taka rawar gani a mulkinsa wajen tunkarar matsalolin da suka shafi tabarbarewar tsaro.
- Tattalin Arzikin Sin Ya Kara Samar Da Dama Ga Bunkasuwar Sauran Kasashen Duniya
- Bangaren Sin: Ya kamata Al’ummar Kasa Da Kasa Ta Goyi Bayan Kasashen Yankin Manyan Tabkuna Wajen Gina Makomar Bai Daya
Ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Nijeriya fiye da yadda ya same ta a lokacin daya amshi kambun mulki a watan Mayu shekarar 2015.
Adesina tsohon babban Editan Jaridar Sun wanda aka nada shi a matsayin mai magana da yawun Shugaban kasa a watan Mayu na 2015 lokacin da Buhari ya hau kan karagar mulki watan Mayu 2015, an sake nada shi kan mukamin a karo na biyu watan Agusta 2019 bayan an sake zaben Buhari a wa’adinsa na biyu.
Da ake hira da shi a shirin gidan Talbijin na Channels mai taken ‘Suyasa Ayau’,Adesina ya ce babban aikin da maigidan shi ya yi ba wani shakku dangane da hakan.
“A shekarar 2015 kowa ya san inda Nijeriya take domin akwai kananan hukumomi 17 da suke karkashin ‘yan ta’adda kamar yadda ya bayyana”.
Da aka tambaye shi ko an samu wani cigaba sai ya ce,“da akwai ci gaba.Yawansu na raguwa sannu a hankali a shekaraun da suka gabata yanzu abin ya zama tarihi babu wani wanda zai canza al’amarin”.
Bugu da kari yayi karin bayani kan nada mukaman Shugabannin rundunonin tsaro wanda kamar yadda yace abin ba abin tafarkin samun daidaituwa,ko kuma al’ amari mai nasaba da kabilanci ko yin abinda ya dace.Shugaban kasa Buhari yana da dama ya nada wadanda yake ganin za su iya aikin na kwato Nijeriya daga hannun ‘yan ta’adda.
“Kar ku hada al’amarin tsaro da kabilanci kada ku hada shi da sai an biya hakkin kowa,maganar gaskiya yana da damar ya nada duk wanda yaga ya dace mukami.Maganar gaskiya tsarin mulkin da yayi magana kan ayi abu ba tare da wata mina- mina ba shi yaba Shugaban kasa dama ta cewa yana iya ba duk wanda yaso mukami”.
Buhari da yake daga Jihar Katsina yake sashen Arewa maso yamma ana ganin laifinsa domin yadda ya fifita ‘yan Arewa a wurin bada mukamai.Watan Nuwamba na shekarar data gabata lokacin da ake kamfen na zabubbukan 2023, dantakarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar,ya ga laifin Shugaban kasa Buhari kan abinda ya kira da sauran aiki na yadda ya bada mukaman Shugabannin rundunonin tsaro,ya ce masu jagorancin hukumomin da suka shafi tsaro daga Arewa su ke.
Ko da aka nuna masa alkalumma da ba na kunbiya- kunbiya ba da ke nuna tsakanin watan Mayu 2015 da Mayu na 2022, ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane,’yan bindiga dadi sun kashe ‘yan Nijeriya fiye da 55,000.Adesina ya dage ne da cewa Shugaban kasa zai bar halin tsaro cikin sauki fiye da yadda ya samu al’amarin ba a cewa komai a shekarar 2015.Yana cewa lokacin da Buhari ya fara mulki akwai ‘yan ta’adda da suka mamaye fadar wasu Sarakuna a wasu sassa na Arewa.
Kamar yadda ya jaddada, “Abinda nake nufi da su suke kulawa da fadar Sarakunan shine’ fadar da suke zama ofisoshi ne na Shugabannin kananan hukumomi.Hukumar masu bautawa kasa bata iya ko kiran dalibai da suka kammala jami’oi, kai ba ma su iya tura wadanda suka kammala jami’a wadancan wuraren don aikin yi wa kasa hidima.
Sai yayi tambaya akan “Abinda ke faruwa ke nan yanzu? Ba haka bane Sarakunan sun dawo fadarsu hakanan ma Shugabannin kananan hukumomi sun koma ofisoshin su.Hukumar kula da al’amuran masu bautar kasa NYSC suna kiran wadanda suka kammala makarantu a ofisoshinsu na Jihohi, ana kuma tura su wadancan Jihohin.Ko yanzu za a iya cewa babu wani cigaban da aka samu.Don Allah mu bayyana gaskiya idan ita ce ta kasance ba wani boye- boye.”
Kan maganar maganar jiragen fadar Shugaban kasa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai fadi zai sayar da su ba lokacin da yake kamfen a shekarar 2015.
Hakanan ma Adesina yace Bishop na katolika Diocese ta Sakkwato Matthew Hassan-Kukah wanda ya bayyana cewa Shugaban kasa yayi alkawarin yin hakan kafin zaben shi.
Rahoton LEADERSHIP ya bayyana Kukah bayanin sakon da yayi na Ista ta 2023 har ila yau ya sake yi ma Shugaban yarfe inda yace,”Yayin da kake shirin komawa Daura ko Kaduna,bana jin kai a matsayinka kana ganin ka cimma duk wadansu kudurorin da kayi niyyar cimmawa,wato kamar kawo karshen ta’addanci tare da murkushe al’amarin rashawa,dawo da ‘yan mata,kai na kowa ne kamar yadda kake ba na kowa ba,sayar da Jiragen saman Shugaban kasa ka rika tafiya damu, dadaisauran wasu abubuwa.
Da yake maida martani kan suki- burutsun da Kukah ya yi Adesina ya ce shi mai wa’azin kirista ya cika sa siyasa a al’amuranshi domin duk wadansu hujjojinsa ya mamaye su da kalaman siyasa.
“Shi (Kukah) ya yi magana kan sayar da Jirginn Shugaban kasa,an taba yin wannan alkawarin?Kun san cewa a shekarar 2015,an bayyana wasu alkawura da aka yi da su ‘yan takarar basu sani ba.Don haka ta yaya zai fara soki- burutsun cewa yayi alkawarin hakan?”jami’aun al’amuran yada labarai na Shugaban kasa ya tambaya.
“Maganar sai da Jirgin Shugaban kasa kamata yayi shi (Kukah) ya bayyana alkawarin da Shugaban kasa yayi.Shugaban kasa yayi alkawari ne na zai duba yadda al’amarin yake ya kuma yi hakan an bada helikwabtoci ga sojojin sama sai kuma wasu helukwafta biyu zuwa uku da aka sayar,”.
Ya ce akwai maganar lura da kudaden da ake kashewa wajen lura da su helikwaftoci inda aka sayarda duk helikwaftocin abinda wasu basu amince da shi ba inda za a fara amfani da Nigerian Airways da har yanzun akwai shi.
Dangane da yaki da cin hanci da ta’addanci Adesina yace Buhari yayi kokarin shi a al’amarin tsaro da maganin rashawa,inda ya kara da cewa Nijeriya ba haka take ba a shekarar 2015 lokacin da Shugaban kasa ya hau kan karagar mulki.
“Shin muna kan al’amarin ta’addanci a shekarar 2015? ba’a ma kai ga gamawa da al’amarin gaba daya ba, amma ai ba muna inda muka samu kanmu ba?Idan Baba Kukah zai yi ma kan shi adalci da kiran da yake yi, ya dace ya tuna da cewa wannan kasa tamu Nijeriya ba haka take ba kamar a shekarar 2015,”.