Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ta ce ta kama wasu ‘yan bindiga biyu a ranar Alhamis a Kano tare da kwato tarin makamai da alburusai.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dokta Peter Afunanya, ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
- Da Dumi-Dumi: Sarkin Musulmi Ya Ayyana Juma’a A Matsayin Ranar Sallah
- Bunkasuwar Kasar Sin Mai Inganci Ta Ingiza Kwarewar Jama’arta
Afunanya ya ce ‘yan sandan sun kama bindigu kirar AK-47 guda biyu da harsasai.
Ya ce wadanda ake zargin suna kan hanyar wucewa ne domin kai makaman da za su kai hari a daya daga cikin Jihohin Arewacin Nijeriya.
Wannan ci gaban, a cewarsa, yana nuna bukatar ‘yan kasa su kasance cikin taka-tsan-tsan tare da kai rahoton duk wani yunkuri, mutane ko wani abu da ba a saba gani ba ga hukumomin tsaro mafi kusa da su.
“An umarci ma’aikata da masu da baki da cibiyoyin yawon bude ido da su yi taka-tsan-tsan a lokacin bukukuwan sallah.
“Ya kamata su kara daukar matakan tabbatar da tsaron wurarensu.
“Duk da haka, muna yi wa Musulmi masu aminci, fatan zaman lafiya da murnar bukukuwan sallah karama.
“Mun yi alkawarin yin aiki tare da hukumomin ‘yan uwa da sauran masu ruwa da tsaki don samar da ingantaccen tsaro a lokacin da kuma bayan bukukuwan sallah karama,” in ji shi.