Wani basaraken gargajiya a garin Aghara, da ke Karamar Hukumar Kabba-Bunu a Jihar Kogi, ya mutu a hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da shi.
Rahotonni sun ce basaraken mai suna David Obadofin, ya shafe kwanaki 12 a hannun ‘yan bindiga bayan da suka yi garkuwa da shi.
- Tanzaniya Ta Yi Maraba Da Zuwan Tawagogin Yawon Shakatawa Na Sin
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’addan Boko Haram 35, Sun Tarwatsa Sansanoni 12 A Dajin Sambisa
Wani mutum daga cikin iyalan basaraken ya ce ya mutu ne sakamakon azabtar da shi da masu garkuwan suka yi.
Wata majiya ta bayyana cewa wadanda suka sace basaraken sun nemi a biya su Naira miliyan biyu kafin su sake shi tare da wata budurwa mai suna Temidayo Elewa.
Bayanai sun ce basaraken ya mutu ne kafin a biya kudin fansar.
‘Yan bindigar sun sace basaraken – wanda hamshakin manomin kashu ne, tare da Elewa a ranar bikin Easter a gidansa da ke Aghara da misalin karfe 11 na dare, inda suka bukaci a biya kudin fansa har Naira miliyan 60 domin sakin su.