An rahoto cewa, an kashe sojoji biyu da wasu mazauna karkara 15 a yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a yankuna uku da ke karamar hukumar Apa a jihar Benuwe.
Wasu mazauna a yankin sun ce, an kai harin ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Talata a yankunan uku na Opaha, Odogbo da Edikwu.
Wani mazaunin yankin mai suna Kole ya bayyana cewa, an gano gawarwaki 17 ciki har da na sojojin biyu na rundunar OPWS, inda ya ce, an gano gawarwakin ne a wani Daji da safiyar ranar Laraba.
Ya ce, daya daga cikin sojojin da aka kashe, kwamanda ne, ya rasa ransa ne yayin da ya tunkari ‘yan bindigar a bisa kokarinsa na dakile harin da suka kawo a yankin.
Da aka nemi jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ta OPWS, lutanan DO Oquah, ya ce baya gari amma zai yi cikakken bayani daga baya.
An yi kokarin jin ta bakin Kwamandan shiyya na rundunar OPWS da ke kula da karamar hukumar Apa, Mejo Ogundile ta wayar tarho amma hakan ya ci tura.
Har ila yau, an tuntubi kakakin rundunar ‘yansanda ta jihar, Catherine Anene, inda ta ce, bata da masaniya kan afkuwar lamarin.