Da sanyin safiyar yau Asabar ne rukunin farko na Sinawa da aka kwaso daga kasar Sudan ta jirgin sama, su sama da 340 suka sauka a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin.
Kafin isowarsu birnin Beijing, Sinawan sun taso ne daga filin jirgin saman kasa da kasa na Sarki Abdulaziz dake birnin Jeddah na Saudiyya da daren jiya Juma’a. Wannan rukuni dai bangare ne na jimillar Sinawa 817 da suka isa tashar jiragen ruwan birnin Jeddah a ranar Alhamis, kamar dai yadda mukaddashin jakada a ofishin jakadancin Sin a Saudiyya Yin Lijun ya bayyana.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce sama da Sinawa 1,300 ne aka yi nasarar kwashewa daga kasar Sudan, tun bayan da ofishin jakadancin Sin dake kasar ya sanar da fara gudanar da aikin.
Kaza lika ma’aikatar ta ce har yanzu, akwai Sinawa kalilan dake zaune a kasar ta Sudan, kuma gwamnatin Sin za ta samar musu dukkanin tallafin da suke bukata.
Bugu da kari, kakakin rundunar sojojin ’yantar da al’ummar kasar Sin ko PLA a takaice, Tan Kefei, ya sanar a yau Asabar cewa, daga ranar 26 zuwa ta 29 ga watan Afrilun nan, wasu jiragen ruwan yaki 2 na kasar Sin sun kwashe ’yan kasar Sin 940, da karin wasu ’yan kasashen waje 231 daga Sudan zuwa birnin Jeddah na kasar Saudiya. (Saminu Alhasan, Bello Wang)