Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sayo motoci masu aiki da lantarki, inda ya ce “matakin na nufin mazauna Legas za su daina aiki da man fetur su soma amfani da makamashi mai tsafta.”
Gwamnatin Jihar Legas ta ce ta sayo sabbin motoci masu amfani da larntarki da zummar yin aiki da su a matsayin motocin haya.
- ‘Yan IPOB 9 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Kashe ‘Yansanda A Imo
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3, Sun Kwato Makamai A Zamfara
Gwamnan Jihar, Babajide Sanwo-olu ne ya bayyana haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi.
Ya ce an sayo motocin ne da zummar saukaka sufuri da kuma sake tasirin sauyin yanayi a Legas, birni mafi girma a Afirka da ke da mutane fiye da miliyan 15.
Wannan ne karon farko da hukumomi a Nijeriya suka sanar da sayo irin wadannan motoci domin yin sufuri.
Sanwo-Olu ya ce matakin zai tabbatar da ”tsaftace tsarin sufuri” a jihar.
”Sabbin motocinmu masu aiki da lantarki za su inganta sufuri da kuma rage gurbata muhalli.
Hakan na nufin mazauna jihar za su yi murna da amfani da man fetur sannan su yi maraba da makamashi mai tsafta,” a cewar gwamnan a sanarwar da ya fitar.
Kawo yanzu ba a san adadin motocin da gwamnatin ta saya ba, amma Sanwo-olu ya ce za a karo motoci masu yawa da ke aiki da lantarki don inganta sufuri a jihar
Ya kara da cewa nan da watanni masu zuwa za a soma amfani da motocin a “matakin gwaji.”
A cewarsa hakan zai bai wa gwamnati damar ”tattara isassun bayanai game da aiki da makamashi maras gurbata muhalli” da kuma kwatanta shi da yadda ake sufuri da masu aiki da fetur da zummar inganta tsarin sufuri.
Mutanen jihar sun yi maraba da wanna mataki ko da yake wasu sun nuna dari-dari game da dorewarsa ganin yadda shirye-shirye da dama da gwamnatoci ke bijirowa da su suke lalacewa.
Nijeriya ta yi kaurin suna wurin dauke wutar lantarki don haka mutane ke ganin zai yi wahala matakin ya dore.
Wasu kuma sun bayyana cewa cunkoson ababen hawar da ake fama da shi a Legas zai zama kalubale ga wannan shiri.
Sai dai gwamnati ta ce za ta samar da “tashoshin da za a rika yin cajin motoci masu aiki da lantarkin.”