Dakarun Operation Hadin Kai sun ceto wasu ‘yan mata biyu da aka sace daga karamar hukumar Chibok ta Jihar Borno a watan Afrilun 2014.
Wannan ceton ya zo ne shekaru tara da ‘yan ta’addar Boko Haram suka kai hari makarantarsu a lokacin da suke rubuta jarabawar kammala sakandare.
- A Yi Kokarin Yin Amfani Da Damammakin Da Kasar Sin Ta Samar
- Jarin Waje Na Sin Na Bunkasa Ci Gaban Kasar Habasha
An kula da wadanda abin ya shafa – Esther Marcus da Hauwa Malta, dukkansu masu shekaru 26 – yayin da sojoji suka ceto su a Lagara, wani yanki na ‘yan Boko Haram da ke dajin Sambisa, a ranar 21 ga Afrilu, 2023.
Ceton na baya-bayan nan, adadin ‘yan matan da aka yi garkuwa da su yanzu ya kai 125, ciki har da 107 da ‘yan ta’addan suka sake su a shekarar 2018, uku da sojoji suka ceto a shekarar 2019, biyu a shekarar 2021, da kuma 11 a shekarar 2022.
A cewar kwamandan Operation Hadin Kai, Manjo Janar Ibrahim Sallau Ali, “har yanzu ba a gano 94 ba.
“An ceto Esther tare da ‘yarta ‘yar shekara daya. Yayin da ake garkuwa da ita, ta auri wani Garba, wanda ake kira Garus, dan ta’adda, wanda daga baya sojoji suka kashe; sannan wani dan ta’adda mai suna Abba ya aure ta; tana tare da shi har zuwa lokacin da aka ceto ta.”
Kwamandan ya bayyana cewa an ceto Hauwa Malta da cikin wata takwas da kwana 10; ta kara da cewa ta haifi wani yaro a cibiyar lafiya ta Seven Div kwanaki 10 bayan ceto su.
Sojojin sun kuma kashe sama da mutane 70 da ake zargin ‘yan ta’adda ne a farmakin da suka kai a yankin Arewa maso Gabas.
An kuma kama sama da ‘yan ta’adda 140 a tsawon lokacin, tare da kwato makamai da dama da suka hada da nakiya, kamar yadda daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis.